Shugaba Bassirou Diomaye Faye dai na ta kokarin samar da tattaunawa kan kwangilolin mai da iskar gas. Hoto / fadar gwamnatin Senegal

Senegal ta shiga jerin ƙasashe masu arzikin man fetur a ranar Talata inda a bangare guda ƙungiyar Woodside Energy ta Australia ta sanar da cewa ƙasar wadda ke yakin Afirka ta Yamma ta soma haƙar mai a aikin farko na teku.

Duk da cewa babu tabbas kan yawan man fetur din da Senegal za ta dinga haƙowa ya kai yawan manyan kasashe masu arzikin man fetur kamar Nijeriya ba, amma ana kyautata zaton cewa sashen masana'antar man da iskar gas din za ta kawo biliyoyin kudaden shiga ga gwamnatin ƙasar tare da samar da sauyi ga tattalin arzikinta.

"Wannan rana ce mai cike da tarihi ga Senegal da kuma Woodside," in ji shugaban kamfanin, Meg O'Neill, yana mai cewa haƙo "man fetur na farko" daga filin Sangomar "wani muhimmin abu ne".

Zurfin wurin haƙar man ya kai kilomita 100 (mil 60) daga gabar tekun, sannan jirgin dakon man na iya tara ganga miliyan 1.3, in ji Woodside.

Iskar gas

Aikin ruwan mai zurfi zai samar da ganga 100,000 na mai a kowace rana, kana wurin na ƙunshe da tsantsar iskar gas.

Woodside yana da kashi 82 cikin 100 na hannun jarin aikin ruwan mai zurfi kana ragowar kuma na kamfanin makamashi mallakar gwamnatin Senegal Petrosen ne.

Kasashen Afirka da dama na ci gaba da gudanar da ayyukan mai da iskar gas duk da matsin lamba da kasashen duniya ke yi na kawar da gurbataccen mai da ke haifar da iska mai dumama yanayi.

AFP