Rasha ta saka sunan kamfanin Meta na Amurka a jerin sunayen “Yan ta’adda da masu tsaurin ra’ayi”

Rasha ta saka sunan kamfanin Amurka na Meta, kamfanin dake da mallakin Instagram da Facebbok a jerin sunayen kungiyoyin “ta’adda da tsaurin ra’yi”, kamar yadda shafin yanar gizo na Aiyukan Tarayya na Sanya Idanu Kan Sha’anin Kudade.

Matakin da aka dauka a ranar Talata ya saka Meta a jerin sunaye tare da kuniyoyi masu tsaurin ra’ayi, ‘yan ta’addar kasashen waje da ‘yan adawa da gwamnatin Rasha.

A karshen watan Maris ne Rasha ta hana amfani da Facebook da Instagram saboda “Yada ra’ayin aiyukan masu tsattsauran ra’ayi” bayan da mahukuntan kasar suka zargi Meta da aminta da “Russophobia” (Kyama ko tsoron Rasha) a lokacin da Rasha ta fara kai hare-hare a Yukren.

A ranar 10 ga Maris ne Meta ya sanar da cewa shafukansu za su bayar da damar a dinga rubuta jinloli irin su “mtuwa ga masu mamaya ‘yan Rasha”, amma wannan abu zai bayu ne ga masu rubutu daga cikin kasar Yukren kawai.

‘Yan rasha sun koma amfani da VPN don ci gaba da amfani da shafin na yanar gizo.

Instagram ya yi shuhura sosai a Rasha, kuma ya zama babban dandalin yin tallace-tallace.

Biliyoyin mutane ne ke amfani da manhajar ta Meta a duniya.

AFP