NNPC ya ƙaryata rahoton zargin ya yi karin naira tiriliyan 3.3 a kudin tallafin man fetur / Hoto: Reuters

Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC) ya ƙaryata wani rahoto da kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka yaɗa wanda ke zarginsa da yin ƙarin Naira triliyan 3.3 a kuɗin tallafin man fetur na gwamnatin tarayyar Nijeriya.

NNPC ya ce yana gudanar da harkokin kasuwancinsa ne bisa ga gaskiya da amana ta hanyar bin ƙa'idojin ƙasashen duniya kana babu wani lokaci da ya taɓa ƙara kuɗin tallafin man fetur na gwamnatin tarayyar Nijeriya, kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X.

Sanarwar wadda ke dauke da sa hannun babban jami’in hulda da jama’a na Kamfanin Olufemi Soneye, ta bayyana cewa, duk wani tallafin man fetur da kamfanin ya yi a baya, an tattara bayanai da takardunsu kana an mika zuwa ga hukumomin da suka dace.

"NNPC ba shi da masaniya game da wani bincike kan kuɗaɗen da ya kashe wajen ba da tallafin mai ko wani bincike da ya biyo baya, don haka a takaice kamfanin na fatali da zargin 'yan jarida da kuma gidajen yaɗa labarai mabambanta,'' in ji sanarwar.

Kazalika sanarwar ta ce “NNPC Ltd zai bijire wa duk wani yunƙuri na janyo kamfanin cikin siyasa ta tallafin man fetur domin a halin yanzu yana gudanar da harkokin kasuwanci bisa tanadin dokar masana’antar mai ta (PIA).''

Kamfanin NNPC ya yi kira ga 'yan jarida da kafafen yaɗa labarai kan su tabbatar da cewa sun gudanar da sahihin bincike tare da tantance bayanai kafin su yaɗa domin kiyaye ƙa'ida da dokokin aikin jarida don guje wa yaudarar jama’a.

TRT Afrika