Hukumar ta ce ta gana a makon da ya gabata da masu samar da fetur da masu tace shi. / Photo: AFP

Hukumar kula da albarkatun man fetur ta Nijeriya ta ce a ranar Litinin din nan za ta hana izinin fitar da man fetur ga masu samar da man da suka kasa cika ka’idojin da aka gindaya musu na samar da man ga matatun mai na cikin gida, ciki har da matatar Dangote, wadda ita ce mafi girma a Afirka.

Dokar masana'antar mai ta Nijeriya, ta umurci masu samar da mai da suka hada da kamfanonin mai na kasa da kasa da su sadaukar da wani takamaiman adadin danyen mai ga matatun cikin gida kafin a fitar da shi zuwa kasashen waje, wata bukata da ake kira wajibcin samar da danyen mai a cikin gida.

Sai dai masu samar da mai sun ce ba su bi wannan ka’ida ba saboda matatun man ba sa saya akan farashi mai kyau.

Hakan ya sa matatar man Dangote kira ga hukumar da ta tabbatar da wannan doka. Wata sanarwa a ranar Litinin din da ta gabata daga shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya, Gbenga Komolafe, wadda ya rubuta wa kamfanonin hakar mai da cewa ya tunatar da su alhakin da ya rataya a wuyansu da kuma hukuncin da aka tanada kan hakan.

Hukumar ta ce ta gana a makon da ya gabata da masu samar da fetur da masu tace shi.

A wajen taron, masu aikin tace man sun zargi masu samar da shi da rashin mutunta nauyin da ya rataya a wuyansu na samar da kayayyaki, yayin da masu samar da man suka ce matatun ba sa bayar da farashi mai kyau, wanda hakan ya tilasta musu binciko wasu kasuwanni, in ji Komolafe a cikin sanarwar.

Komolafe ya yi gargadi cewa "karkatar da danyen mai wanda aka kebe don matatun mai a cikin gida ya saba wa doka kuma daga yanzu hukumar za ta hana izinin fitar da danyen man da aka kebe don tacewa a cikin gida."

A farkon rabin shekarar 2025, matatun man Nijeriya sun ce za su bukaci ganga 770,500 na danyen mai a kowace rana, inda aka yi hasashen matatar Dangote za ta bukaci ganga 550,000, a cewar wani jadawalin da hukumar kula da mai ta wallafa

Reuters