In low-income countries, the multinationals’ portfolios rated 1.8 on the system. In high-income countries, where more products were tested, they were 2.3. / Photo: Reuters Archive

Wasu manyan kamfanonin duniya kayayyakin abinci da na sha suna sayar da abinci marasa inganci a ƙasashe matalauta idan aka kwatanta da ingancin kayayyakin da suke sayarwa a ƙasashe masu arziki, kamar yadda wani rahoto ya bayyana.

Kayayyakin da kamfanoni waɗanda suka haɗa da Nestle da Pepsi da Unilever suke sayarwa na daga cikin kayayyakin da ƙungiyar Access to Nutrition Initiative (ATNI) ta yi bincike a kansu kuma ta wallafa binciken.

Ƙungiyar ta gano cewa a cikin kamfanoni 30, kayayyakin da ake sayarwa a ƙasashe matalauta ba su samu maki mai kyau ba idan aka kwatanta da waɗanda ake sayarwa a ƙasashen da suka ci gaba.

A yanayin yadda ake bayar da maki ga kayayyaki masu inganci, ana bayar da maki har zuwa biyar dangane da ingancin lafiyar kayayyakin, inda idan maki ya wuce 3.5, ana ɗaukarsa a matsayin wanda ingancinsa aka aminta da shi.

“A bayyane take cewa kayayyakin da wadannan kamfanoni ke sayarwa a kasashe mafi talauci a duniya, inda a nan suka fi ƙarfi ba kayayyaki bane masu inganci sosai ba,” in ji Mark Wijne, daraktan bincike a ATNI, a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wannan ne karo na farko da wannan ƙungiyar ke yin bincike dangane da ingancin kayayyaki a ƙasashe matalauta da kuma masu arziƙi.

Matsalolin cutar kiɓa

Ƙungiyar ta ATNI ta bayyana cewa wannan binciken yana da matuƙar amfani sakamakon abicin da ake sayarwa a cikin gwangwani da kwalba na taka muhimmiyar rawa wurin jawo ciwon ƙiba wanda a halin yanzu ake fama da shi a duniya.

Fiye da mutum biliyan ɗaya a duniya ke fama da ciwon ƙiba, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar..

Bankin Duniya ya yi ƙiyasin cewa kaso 70 cikin 100 na jama'ar duniya waɗanda ke fama da matsananciyar ƙiba na zaune ne a ƙasashe masu tasowa da matalauta.

TRT World