Jirgin kamfanin FAA Boeing / Hoto: AP

Kamfanin jiragen sama na Boeing ya cim ma kudurin kera jirage inda a shekarar 2023 ya samu karin kashi 70 cikin 100 na jiragen da ya kera, lamarin da ya nuna karara yadda ake yawan tafiye-tafiye da kuma bukutun da ake da su na jiragen sama, yayin da abokin hamayyarsa a kasuwanci na Turai Airbus ya kasance kamfanin da ya fi kera jiragen sama masu yawa a tsawon shekara biyar babu fashi.

A ranar Talata ne Boeing ya fitar da alkaluman karshen shekarar 2023, hakan na zuwa ne bayan wani hatsari da jirginsa kirar Alaska 737 MAX 9 ya yi, sakamakon fitar da wani bangarensa ya yi lokacin da yake tafiya a makon jiya.

Kamfanin jirgin na Amurka ya kera jirage 528 a shekarar 2023 sannan ya samu sabbin oda guda 1,314 baya ga izinin sokewa da ya bayar.

Wannan kari da ya samu daga 480 da odar 774 a shekarar 2022, na zama shekara uku kenan da ya fi samun nasara.

Kazalika kamfani ya kera kananan jirage 396 kirar jet 737 a bara, wanda ya cim ma burin da aka sabunta na kera kananan jirage akalla 375 sai dai bai iya cim ma burin samar da kananan jirage 400 zuwa 450 ba.

A watan Oktoba ne kamfanin ya rage adadin jirage da ya yi kudurin kerawa bayan da masana'antar samar da kayayyakin hada jirage Spirit AeroSystems ta tilasta masa duba jiragensa, lamarin da ya rage ayyukan jigilar kayayyaki.

Boeing ya kera jirgin Dreamliner 787 guda 73 a shekarar 2023, inda ya kai ga cim ma burinsa na kera jirage 70 zuwa 80.

Sai dai duk da wannan nasara da Boeing ya samu kamfanin Airbus na Turai ya doke shi, inda ya zarce alkaluman masana'antu tare da zarta alkaluman kera jirage 720 a shekarar 2023 da jirage 735 da ya samar, a cewar majiyoyi.

Jirgin Airbus ya yi zarra

Bisa alkaluman kamfanin Airbus na watan Janairu zuwa Nuwamban 2023 kadai, kamfanin na Turai ya yi zarra a matsayin da yake kai tsawon shekara biyar kenan.

Game da cikakkun alkaluman shekara na Boeing da kuma jirage 735 na Airbus da masana'antu suka ambato, kason kasuwar Boeing da abokin hamayyarsa yana kan kaso 42 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 50 cikin 100 kafin matsalar dakatar da kera kananan jiragen MAX a shekarar 2019.

A watan Disamba, kamfanin Boeing ya samu adadin oda 371, ciki har da kasuwa mafi girma da ya samu a kowane wata na siyar da jirage 301 kirar 737 MAX.

Kamfanin ya samar da jirage 44 kirar 737 MAXs da kuma tsofaffi samfurin 737NG a watan da ya gabata. Haka kuma ya mika jirage bakwai kirar 767. Sannan odar jiragen da ke kansa sun karu daga 5,324 zuwa 5,626.

Nan gaba a ranar Alhamis an shirya kamfanin Airbus zai fitar da sanarwa kan odar jirage da kuma wadanda zai kera.

Kazalika ana sa ran shugabannin kamfanin Boeing za su fitar da sabbin manufofin shekarar 2024 ranar 31 ga Janairu.

TRT World