Kamfanin Twitter ya takaita adadin sakon da masu amfani da shafi za su iya gani a kullum, da zummar rage "yin almubazzaranci" da sakonni da kuma yin abin da bai dace ba, a cewar shugaban kamfanin Elon Musk.
Ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.
An takaita sakon da shafukan da aka tantance wato verified accounts za su iya gani a kullum zuwa guda 6,000, in ji Musk, inda ya kara da cewa shafukan da ba a tantance ba kuwa, wato unverified accounts ba za su ga sakonnin da suka wuce 600 ba a kullum, yayin da sabbin shafukan da ba a tantance ba za su ga sakon da bai zarta 300 ba.
Nan gaba za a kara adadin da kowanne bangare na masu shafin Twitter za su iya gani, inda masu shafin da aka tantance za su iya ganin sakon da ya kai 10,000, wadanda ba a tantance ba su ga sako 1000 yayin da sabbin shafukan da ba a tantace ba za su iya ganin sako 500, a cewar Musk.
A baya, Twitter ya sanar cewa akwai buktar mutum ya bude shafi a manhajar kafin ya iya ganin sakon da wani ya wallafa, matakin da Musk ya ce na "takaitaccen lokaci ne."
Musk ya ce daruruwan kamfanoni na kwakulo bayanai "sosai" daga Twitter, lamarin da ke tasiri wurin bai wa masu amfan ida shafin zabi na ganin abin da suke so ko akasin haka.
Tun da fari, Musk ya bayyana rashin jin dadinsa game da kamfanonin kirkirarriyar basira wato artificial intelligence [AI] irin su OpenAI, wanda ya mallaki manhajar ChatGPT, wanda ke amfani da bayanan da ya samu a Twitter wajen koya wa mutane magana ko mu'amala da irin tsarinsa.