An bar Afirka a baya a lokacin da Kirkirarriyar Basira ke kawo makudan kudade

An bar Afirka a baya a lokacin da Kirkirarriyar Basira ke kawo makudan kudade

Ana tsammanin kasashen Afirka za su samu kaso mafi kankanta a wadannan kudade.
Kasashen Yamma na kan gaba wajen cin moriyar Kirkirarriyar Basira / Photo: Getty Images

Wani rahoto da Cibiyar MacKinsey ta fitar ya bayyana cewa Kirkirarriyar Basira (AI) na iya samar da kudin shiga daga dala biliyan 2.6 zuwa dala biliyan 4.4 a kowacce shekara, kamar yadda Jaridar Business Day ta Nijeriya ta ruwaito.

Amma wannan kudin fa zai dinga tafiya kasashen da suka ci gaba ne, bayan da tuni suka samu matsuguni a kasuwar Kirkirarriyar Basira.

Ana tsammanin kasashen Afirka za su samu kaso mafi kankanta a wadannan kudade.

Rahotanni sun bayyana misalin yadda Amurka ke da manyan kamfanonin fasaha da ke cikin kasuwar Kirkirarriyar Fasaha.

Sun hada da: ‘OpenAI’ da suka kirkiri ‘ChatGPT’ wanda Microsoft ke daukar nauyi, da kamfanin Google wadanda suka kirkiri ‘Bard’.

Amurka ce ke kan gaba wajen shirin samar da Kirkirarriyar Basira da maki 85.72 a 2022, in ji wani rahoto da Cibiyar Nazarin Tattalin Arzikin Afirka.

Singapore na da maki 84.12 yayin da Ingila ke da maki 78.54, sun zama kasashe uku da ke kan gaba a duniya a wannan fanni.

Ga dukkan alamu Afirka kuma ba ta shirya wa samun wani kaso mai tsoka daga dala tiriliyan 4.4 da Kirkirarriyar Basira za ta samar ko take samarwa ga tattalin arzikin duniya ba.

Yankin Afirka na da maki mafi karanaci na 29.38 a alkaluman da aka fitar.

Rahoton na MacKinsey ya kuma bayyana yadda kasashen Afirka da dama ke can kasa, a jerin kasashen duniya da ake dama wa da su a wannan fanni na Kirkirarriyar Basira.

McKinsey sun kara da cewar duk da kudaden da ake ware wa don ayyukan Kirkirarriyar Basira ba su da yawa, amma kuma bangaren na karfafa da karfafuwa cikin kankanin lokaci.

McKinsey sun kuma bayyana cewar ana tsammanin habakar Kirkirarriyar Basira zai zama irin ta fashar kere-kere ta zama.

TRT Afrika da abokan hulda