Indiya ita ce kasa mafi girma wajen amfani da samar wa da kuma fitar da kayan yaji a duniya . / Hoto: Reuters    

Aƙalla kashi 12 cikin 100 na samfuran kayan ƙamshin da aka yi bincike a kansu ne suka gaza cika ƙa'idoji inganci da aminci da aka gindaya, a cewar bayanan da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya tattaro daga hukumomin Indiya.

Hakan dai ya biyo bayan matakin da ƙasashe da dama suka ɗauka kan haɗarin kamuwa da cututtuka daga amfani da fitattun samfuran biyu.

Binciken da Hukumar Kula da kuma Kare ingancin Abinci ta Indiya ta gudanar a haɗin kayan ƙamshin na girki ya biyo bayan dakatar da sayar da wasu nau'in samfuran kayan kamfanin MDH da Everest da Hong Kong ta yi a watan Afrilu kan yawan maganin kashe ƙwari da ke cikin kayan ƙamshin.

Daga nan ne sai Biritaniya ta tsaurara matakan sa ido kan duk wani kayan ƙamshi da ke shigowa ƙasar daga Indiya, yayin da ita New Zealand da Amurka da kuma Australia suka ce suna kan gudanar da bincike kan samfuran.

Ko da yake dai kamfanin MDH da Everest sun ce samfuransu suna da aminci da inganci wajen amfani.

Kayan ƙamshin suna daga cikin waɗanda suka shahara a Indiya- ƙasar da ke kan gaba wajen amfani da samarwa da kuma fitar da kayan a duniya.

Ana yawan sayar da kayan ƙamshin a ƙasashen Turai da Asiya da kuma Arewacin Amurka.

Bayanan da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tattaro karkashin Dokar 'Yancin Bayanai ta Indiya, ya nuna cewa a gwajin da aka yi na samfura 474 daga cikin 4,054 a tsakanin watan Mayu da farkon Yuli ba su cika ka'idoji da amincin samar da kayayyakin da aka gindaya ba.

Karkashin bincike

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar tsoron abincin ta shaida wa Reuters cewa babu wata matsala a nau'ikan kayan ƙamshin da ta gudanar da gwaji a kansu, sai dai za ta ɗauki matakin da ya dace kan kamfanonin da aka samu da laifi.

''Za a ɗauki mataki kan samfuran da su take ka'ida,'' in ji hukumar, tana mai magana kan tanadin hukuncin da dokar kasar ta yi tanadi, ba tare da wani karin haske ba.

Cibiyar kasuwanci ta Zion Market Research ta ƙiyasta darajar kasuwar kayan ƙamshin Indiya kan dala biliyan 10.44 a shekarar 2022.

Sannan ana kasafin kuɗin watan Maris da aka yi, an ƙiyasta kayayyakin ƙamshin da ake fitarwa zuwa wasu ƙasashe kan dala biliyan 4.46.

Reuters