Saudiyya ta yi kira ga dakarun aware na Rapid Support Forces (RSF), da su yi gaggawar dakatar da abin da ta kira mummunan take hakkin fararen hula da ake ci gaba da yi, yayin da binciken kasa da kasa ke kara tsananta kan ta'addancin da ake yi a yankin Darfur.
An yi wannan kiran a daren Litinin a lokacin wani zaman tattaunawa a Geneva bayan jawabin Babban Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya kan Hakkokin Bil Adama, Volker Turk, game da tabarbarewar take hakkin bil’adama a ciki da kewayen Al Fasher, babban birnin Darfur ta Arewa, a cewar Hukumar Dillancin Labarai ta Saudiyya.
Turk ya shaida wa zaman cewa alhakin “mugayen laifuka” da aka aikata a Al Fasher yana kan RSF gaba ɗaya tare da abokansu da masu tallafa musu, inda ya kawo misalin hare-hare kan fararen-hula da ababen more rayuwa na fararen-hula.
A cikin wata sanarwa da wakilin dindindin na Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, Jakadan Abdulmohsen bin Khothaila ya gabatar, Riyadh ta yi tir da hare-haren RSF a kan Al Fasher a watan Oktoban 2025.
Ta yi tur da abin da ta bayyana a matsayin hare-hare na laifi kan asibitoci, motocin jigilar agaji, da wuraren fararen-hula, wanda ya yi sanadin mutuwar 'yan gudun hijira da dama, ciki har da mata da yara.
‘Bin dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa’
Saudiyya ta jaddada cewa ya zama wajibi RSF ta bi dokokin jinƙai wajen tabbatar da isar da agaji cikin aminci ba tare da tsangwama ba, tare da kiran ƙungiyar da ta bi dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa.
Riyadh ta kuma sake tabbatar da goyon bayanta ga ƙawancen Sudan, tsaro da zaman lafiya, da kuma kiyaye ingantattun hukumomin gwamnati.
RSF ta ƙwace ikon Al Fasher a ranar 26 ga Oktoban 2025, kuma tun daga nan kungiyoyi na cikin gida da na ƙasa da ƙasa sun zarge ta da aiwatar da kisan ƙare dangi a kan fararen-hula.
Faɗan ya yaɗu a cikin 'yan makonnin nan a jihohin Kordofan na Arewa, Yamma da Kudu a Sudan, inda ya raba dubban mutane da gidajensu suka zama ‘yan gudun hijira yayin da rikici tsakanin RSF da sojin Sudan ke ƙara tsananta.
Gwamnatin Sudan ta kuma zargi RSF da kai hari kan wani jirgin agajin Shirin Abinci na Duniya (World Food Programme) ta amfani da jiragen sama marasa matuƙa (drones) a Kordofan ta Arewa, wanda ya yi sanadin mutuwa da lalata muhimman kayan agaji.
Yaƙin, wanda ya ɓarke a Afrilun 2023 kan shirin haɗa RSF cikin rundunar sojin ƙasa, ya jefa Sudan cikin ɗaya daga cikin mafi munin rikice-rikicen jinƙai a duniya, inda aka kashe dubban mutane kuma aka tilasta kusan mutum miliyan 13 barin gidajensu.




















