Ana sa ran zirga-zirgan jirage daga Kenya zuwa Somaliya  ta kankama a watan Fabrairun shekara mai zuwa./ Hoto: Reuters  

Kamfanin jiragen sama na Kenya Airways ya sanar da dage dakatarwar da ya yi ta tsawon shekaru uku a zirga-zirgar jiragensa zuwa Mogadishu babban birnin Somaliya.

Kamfanin ya bayyana shirin dawo da zirga-zirgar jiragen sama kai-tsaye daga Nairobi zuwa Mogadishu, inda ake sa rai jirgin farko zai tashi a ranar 14 ga watan Fabrairun 2024.

Wannan yunkuri "ya yi nuni da irin karuwar kasuwanci da kuma yawan zirga-zirgar jiragen sama da ake samu tsakanin Kenya da Somalia," in ji babban jami'in kasuwanci da hulda da jama'a na Kenya Airways Julius Thairu a ranar L araba.

Sanarwar na zuwa ne mako guda bayan gagarumar nasarar da Somaliya ta samu ta zama mamba a kungiyar Kasashen Gabashin Afirka (EAC) a ranar Juma'a 24 ga watan Nuwamba a taron kolin shugabannin kasashen da aka yi a birnin Arusha na kasar Tanzania.

Daidaita ka'idojin tafiye-tafiye

Shigar Somaliya cikin kungiyar a matsayin mamba ta takwas na zuwa ne bayan shafe tsawon shekaru 11 da mika bukatunta.

Dawo da zirga-zirgar jiragen saman ba wai zai tsaya kan jigilar mutane ba ne kawai, zai kara bude kofar samun damarmaki na kasuwanci da yawon bude ido tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin ya ce ana sa rai zirga-zirgar jiragen sama kai-tsaye za ta daidaita ka'idojin tafiye-tafiye tare da samar da ingantacciyar hanyar sufuri ga fasinjoji da sauran kayayyaki da ake jigilarsu.

A shekarun baya, an yi takun-saka tsakanin Kenya da Somaliya saboda wasu dalilai da suka hada da takaddama kan iyakar teku tare da zargin Kenya da tsoma baki a harkokin cikin gidan Somaliya da kuma matsalar tsaro a Somaliya.

TRT Afrika