Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ta sanar da cewa za ta zuba jarin dala biliyan 4.5 a shirin makamashi mai tsafta a Afirka.
Ministan Masana'antu da Fasaha na kasar Sultan Al Jaber ya bayyana hakan a ranar Talata a yayin taron sauyin yanayi da kasar Kenya ta karbi bakuncin yi da aka shirya don samar da kudade don yaki da dumamar yanayi.
"Za mu saka dala biliyan 4.5...domin kaddamar da bututun ayyukan samar da makamashi mai tsafta a wannan nahiya mai matukar muhimmanci," a cewar Sultan Al Jaber, wanda ke jagorantar kamfanin makamashi na Masdar, mallakar gwamnati, da kamfanin mai na UAE ADNOC da kuma COP28 a yayin taron.
Shugabannin gwamnati da na masana'antu na daga cikin dubban mahalarta taron da ake gudanarwa a birnin Nairobi, inda yankin Afirka ke bayyana fasaharta a matsayin cibiyar samar da makamashi mai tsafta.
Nan gaba bayan taron ana sa ran a cikin shekarar za a gudanar da taron COP28 a birnin Dubai inda za a mayar da hankali kan muhimman batutuwan da za su bunkasa makamashi a duniya a gaba.
"Idan Afirka ta yi rashin nasara, dukkanmu ne muka yi asara," a gargadin da Jaber wanda shi ne Ministan Masana’antu da Fasahar Zamani na Hadaddiyar Daular Labarawa ya yi.
Jaber ya ce zuba jarin zai mayar da hankali wajen bunkasa GW (gigawatts) 15 na wutar lantarki mai tsafta zuwa nan da shekarar 2030 da kuma "samar da akalla karin dala biliyan 12.5 daga bangarori da gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu."
Ya zuwa shekarar 2022 dai, karfin samar da wutar lantarki a nahiyar ya kai gigawatt 56, a cewar Hukumar Makamashi ta Duniya.
Taron na kwana uku a Nairobi da aka fara a ranar Litinin ya hada shugabannin kasashen Afirka don lalubo hanyoyin da za a bi wajen inganta yanayi mabambanta a nahiyar mai mutum biliyan 1.4.
Kasashe a Afirka dai na fama da matsi sakamakon yawan basussuka da kuma karancin kudi da suka yi mata katutu, duk kuwa da dumbin albarkatun kasa da nahiyar ke da shi, inda jarin kashi uku cikin 100 kawai aka saka daga fannin makamashin duniya a nahiyar.