Zanga-zangar matasa a Kenya ta barke ne a cikin watan jiya inda suka buaci shugaban William Ruto da ya yi murabus./ Hoto: AFP

Kenya ta miƙa sabon shirin tattali arzikin ƙasar ga hukumar asusun ba da lamuni ta duniya IMF kana tana sa ran kwamitin asusun zai duba shi domin samun amincewarsa a taron da za a gudanar a karshen watan Agusta, in ji babban ministan ƙasar.

An tilasta wa Kenya kan ta yi gaggawar samar da sabbin tsarin kashe kudaɗenta bayan zanga-zangar adawar matasa kan ƙarin haraji da gwamnatin Shugaba William Ruto ta yi wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum aƙalla 50.

"Sashen baitulmalin ƙasar ya yi hulda mai ƙarfi da IMF, duk ƙalubalen da muke fuskanta,'' kamar yadda Babban Ministan Kenya Musalia Mudavadi ya shaida wa kwamitin kasafin kuɗi na majalisar.

Ya ce gwamnati ta gabatar da manufofinta na tattalin arziki da shirye-shiryenta ga asusun, kuma hukumar ta IMF za ta duba shi a karshen watan Agusta, in ji bayanan da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito a ranar Talata.

"Muradinmu da kuma fatanmu shi ne, buƙatar Kenya ta samu sakamako mai kyau ta yadda za mu tsallake ƙalubalen da muke fuskanta," in ji Mudavadi ga kwamitin 'yan majalisar.

Reuters