Rukunin kamfanin ƙasar Kenya na KCB Group ya amince ya sayar da bankin da ya mallaka, wato National Bank of Kenya, ga rukunin bankin Nijeriya na Access Group.
Babban Daraktan KCB, Paul Russo, ya faɗa ranar Laraba a wajen taron masu hannun-jari cewa an ƙulla cinikin ne kan kuɗin da ya haura kashi 1.25 na darajar bankin, amma bai ambaci taƙamaiman yawan kuɗin ba.
Ya ƙara da cewa, "Abin da ya dace shi ne amsar tayin na Access Group".
Bayan fitowar labarin wannan ciniki, hannun-jarin KCB Group ya ɗaga sama, da kashi 9.9% cikin 100.
Ƙoƙarin faɗaɗa aiki a Kenya
Tuntuni da ma Access yana gudanar da ƙaramin reshe a Kenya, bayan da ya sayi wani bankin a shekarun baya. Sayan NBK zai taimaka masa faɗaɗa ayyukansa a ƙasar, don cin moriyar haɓakar kasuwanci a yankin gabashin Afirka.
KCB, wanda shi ne bankin ba da rance na biyu mafi girma a Kenya, shi ne a baya ya sayi NBK daga hannun gwamnati, wanda matsakaicin banki ne na ba da rance, a wani shirin ceton banki da Babban Bankin Ƙasa na Kenya ya yi a 2019.
Shugaban KCB Group, Joseph Kinyua ya faɗa wa taron masu hannun-jarin cewa yunƙurin kyautata tagomashin bankin NBK ya ci tura, sakamakon wasu manyan dalilai.
A baya can, KCB ya yi nuni kan cewa a baya dai ya zuba jari a NBK da niyyar riƙe shi na tsawon lokaci.
Sake tunani
Eric Musau, shugaban ɓangaren bincike na bankin Standard Investment Bank da ke Nairobi ya ce, "Sai dai kuma, taƙaitar matakin jarin bankin a shekaru biyu na baya wataƙila shi ya janyo wannan sake tunanin".
A ma'aunin kimanta lalitar jari da darajar kadarori, NBK yana da makin kashi 6.9% cikin ɗari a ƙarshen Satumban baya, wanda adadi ne da ya yi ƙasa da yadda ake buƙata, wato kashi 10.5% cikin ɗari.
Musau ya ce, "(Ko ba a yi haka ba) da sai sun buƙaci ƙara jarin NBK".
KCB, wanda ya samu raguwar riba kafin haraji da kashi 15% cikin ɗari, a bara, inda ta koma biliyan 48.5 a kuɗin Kenya na shillings (wato dala miliyan $367.4m). Kuma bankin ya ce ba zai biya ribar hannun jari don yana so ya alkinta jari.
Alkinta zuba jari
NBK shi ne reshen da ke rukunin kamfanin wanda ya samu raguwar kuɗin-shiga a bara daga shekarar 2022, a cewar Russo.
Russo ya ƙara da cewa, sayar da NBK ga Access zai ba da damar alkinta jarin da KCB ya zuba a kasuwancin NBK cikin shekaru huɗu.
A shekarun baya-bayan nan, KCB Group ya saye bankuna a wasu ƙasashen da ke yankin, ciki har da sayen kashi 85% cikin ɗari na Trust Merchant Bank, a Jumhuriyar Dimukraɗiyar Congo a ƙarshen 2022, wanda ya haifar da matsi a lalitar bankin.