Babban Hedkwatar Bankin raya tattalin arzikin Afirka (AfDB)  da ke birnin Abidjan. Hoto / Reuters      

Ana sa ran tattalin arzikin Afirka zai ƙaru da kashi 3.7 cikin 100 a bana sannan da kashi 4.3 cikin 100 a shekarar 2035 daga kashi 3.1 da aka samu a shekarar 2023, kamar yadda shugaban Bankin Ci gaban Tattalin Arzikin Afirka Akinwumi Adesina ya bayyana a ranar Laraba.

"Tattalin Arzikin Afirka na samun tagomashi duk da tsaikon kalubalen sauyin yanayi da hauhawar farashin kayayyaki a duniya da tashe-tashen hankula da yawan basussuka da dai sauransu,'' a cewar Adesina a taron shekara-shekara na bankin.

Adesina ya ce bankin na daga cikin sauran sassan da ke taimakawa wajen tara dalar Amurka biliyan 3.2 don gina dogon layin jirgin ƙasa a yankin Gabashin Afirka wanda ya haɗa ƙasashen Tanzaniya da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da kuma Burundi.

Kazalika, bankin zai ba da dala miliyan 500 don bunƙasa hanyar Lobito wacce ta haɗa ƙasar Zambiya da Angola da kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

“Muna ƙokarin tara dala miliyan 375 domin samar da hanyar layin dogo wanda zai haɗa Nijeriya zuwa jamhuriyar Nijar,” in ji Adesina.

Haka kuma "Muna haɗa dala biliyan 3.5 zuwa dala biliyan 5 don bunkasa hanyar da za ta hada ƙasashen Laberiya da Guinea," in ji shi.

Reuters