Farashin man fetur ya ƙaru a ranar Litinin a daidai lokacin da kungiyar OPEC ta yanke shawarar ci gaba da rage ɗanyen man da take samarwa har zuwa ƙarshen watan Yuni tare da kira kan a tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.
An sayar da ɗanyen mai samfurin Brent a kan dala 83.78 a kowacce ganga da misalin karfe 07:53 na safe agogon GMT, inda aka samu ƙarin kashi 0.28 cikin 100 daga farashin da aka rufe kasuwar a mokon jiya kan dala 83.55.
A lokaci daya kuma an sayar da samfurin danyen mai na West Texas Intermediate (WTI) kan dala 80.09 a kowace ganga, inda aka samu karin 0.15 cikin 100 bayan da kasuwar ta rufe akan farashin $79.97 a kowace ganga.
Sake nazari
Manyan kasashe da dama a kungiyar OPEC, ciki har da Saudiyya da Rasha, sun amince su tsawaita wa'adin lokacin da suka dauka na rage yawan ɗanyen man da suke fitarwa har zuwa karshen watan Yuni.
Kasashen Saudiyya da Rasha za su rage yawan man da ake samarwa a kullum da ganga miliyan daya da kuma ganga 471,000 ko wannensu, yayin da Iraki da Hadaddiyar Daular Larabawa su ma za su rage yawan ganga 220,000 da kuma 163,000 ko wannensu na man fetur din da suke fitarwa a kowace rana.
A karshen watan Yuni, kasashen za su sake yin nazari kan rage man da suke fitarwa, kana akwai yuwuwar su iya sauya matakinsu bisa ga yanayin kasuwa, a cewar sanarwar OPEC.
Sai dai halin da ake ciki na tashin hankali da ake fuskanta a Tekun Bahar Maliya da kuma kasashen yankin Gabas ta Tsakiya na ci gaba da taka rawa wajen hauhawar farashin mai amma akwai yuwuwar idan aka tsagaita wuta farashin ya sauko ƙasa.
Tattaunawar tsagaita wuta
An soma gudanar da tattaunawar tsagaita wuta a Masar a wannan makon. Tawagogin Hamas da Qatar da kuma Amurka sun isa birnin Alkahira inda suka daura kan wata sabuwar zagayen tattaunawa a ranar Lahadi.
A karshen mako ne, Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza. "Idan aka yi la'akari da irin girman wahalhallun da ake fuskanta a Gaza, dole ne a gaggauta tsagaita wuta na akalla makonni shida masu zuwa, wannan shi ne abin da ke kan teburin a halin yanzu," in ji Harris.
Ana kan kokarin ganin an samu matsaya kafin a fara azumin watan Ramadan, wanda ake sa ran za a soma a cikin watan Maris, kamar yadda wata majiya mai ƙarfi a Masar ta shaida wa kafar yada labarai na Alkahira da ke kasar Masar.
Riba mai yawa
Akwai yuwuwar yawan kudin ruwa a Amurka, kasa mafi girma da ke amfani da man fetur a duniya, na iya rage bukatar man ya sanya matsin lamba kan farashin mai.
Bayan bayanan tattalin arziki da aka sanar a Amurka a makon da ya gabata, ana tsammanin cewa babban bankin Tarayyar Amurka zai fara rage yawan kudin ruwa a farkon watanin rabin shekarar nan.
Masu sharhi sun yi imanin cewa bayanan tattalin arziki na wannan makon a Amurka za su ba da haske game da shawarar da bankin zai yanke a nan gaba.
Masana za su sa ido kan bayanan Shugaban Fed Jerome Powell ga Majalisa a wannan makon.