Shugabannin Afirka na neman amfana da kawancensu da China. Hoto: Fadar Shugaban Kasar Afirka ta Kudu

China na karbar bakuncin taron kasashen Afirka 50 a makon nan da manufar haɓaka alaƙarta da samar da zuba jari.

A yayin da Ƙasashen Yamma suka saka takunmumai ga fitar da kayayyaki daga China kamar motoci masu aiki da lantarki da allunan zuƙar makamashi daga hasken rana, China na bukatar haɓaka kasuwancinta a Afirka.

Shugabannin kasashen Afirka da za su halarci taron na iya jan kafa wajen amsa bukatun China ba tare da samun tabbaci game da alkawuran baya da aka yi musu da kuma ci gaban ayyukan gina kasa da ake yi.

Eric Olander na Shirin China a Kudancin Duniya ya jaddada muhimmancin fahimtar abubuwan da China ke bai wa fifiko.

'Kusantar China'

"Kasashen da cikin tsanaki suka nazarci sauyin da aka samu ne za su amfana da wannan nasara ta China ta hanyar kusantar da bukatunsu ga sabbin abubuwan da China ta baiwa fifiko," in ji Eric Olander, daya daga cikin wadanda suka samar da Shirin China a Kudancin Duniya.

"Wannan babban aiki ne ga nahiyar da ba ta da masaniyar yadda China ta ke."

China na sauya ayyukanta daga manya-manyan ayyuka zuwa ga sayar da muhimman fasahohi na kere-kere ga Afirka. Saboda yadda kasuwanci da Yammacin Duniya ya tabarbare, China na da manufar samun sabuwar kasuwa ga motocinta masu aiki da lantarki da allunan zukar makamashi daga rana.

A shekarar da ta gabata, China ta bayar da bashi sau 13 na dala biliyan $4.2 ga kasashen Afirka takwas da bankunan yanki guda biyu, kamar yadda alkaluman Cibiyar Cigaban Kasashen Duniya ta Jami'ar Boston suka nuna, wanda kimanin dala miliyan $500 ya tafi ga aikin samar da makashi daga ruwa da hasken rana.

Karin kudade don gudanar da ayyuka

China ta sabunta ka'idojin bayar da bashi, tana bayar da kudade da dama ga samar da makamashi mai sabuntuwa da rage yawan kudaden da take bayarwa ga samar da ayyukan da aka saba gani.

Alkaluman baya-bayan nan sun nuna an samu raguwa a basukan da China ke baiwa kasashen Afirka.

Ana sa ran shugaba Xi Jinping zai tallata masana'antun samar da makamashi mai sabuntuwa na China ga taron na shugabannin Afirka. Dukkan shugabannin Afirka za su halarta banda na Eswatini.

Abokan adawar China da suka hada da Amurka, Ingila, Italiya, Rasha da Koriya ta Kudu ma na awrcin kasashen Afirka. Sai dai kuma, yadda China ke zuba jari da bayar da bashin kudade ya sanya an fi baiwa nata taron muhimmanci.

Shugabannin Afirka na son tabbatar da cewa sun amfana da kawancen da kasashensu ke yi da China.

A yayin da China na kan iya zama mai zumudin habaka kasuwanci da samun damar hakan ma'adanai, dole ne ta kula sosai game da bayar da kudade saboda sake fasalin ci da biyan basussuka da matsalolin tsaro.

TRT Afrika