A yayin taronsu na farko a wannan shekara, kwamitin Harkokin Kudi na Babban Bankin Nijeriya karkashin gwamnan bankin CBN, ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 22.75 cikin 100.
Gwamnan bankin ya sanar da hakan ne ranar Talata bayan taron kwamitin da ya gudana a birnin tarayyar Nijeriya, Abuja, inda hedikwatar babban bankin take. An bayyana cewa duka mambobin kwamitin su 12 sun amince da wannan mataki.
A nazarin tattalin arziki, kara kudin ruwa wani mataki ne da ke da manufar janyo hankalin masu ajiyar kudi a bankuna, don su ƙara yawan kuɗaɗen da suke ajiyewa a asusun ajiya da bankuna ke biyan kudin ruwa kan ajiya.
A wani bangaren kuma, kara kudin ruwa yakan rage yawan masu cin bashin banki, wadanda za su ga tsadar cin bashin, musamman idan sun kwatanta da ribar da za su iya samu ta amfanin da kudin bashin don kasuwanci, ko yin wata hada-hadar kudi.
Kafin wannan sabon mataki na CBN, yawan kudin ruwa da aka ƙayyade a kasar shi ne kashi 18.75, tun bayan taron kwamitin da ya gudana a watan Yuli na shekarar 2023.
Da ma dai alhakin babban bankin kasa ne ƙayyade kudin ruwa da bankunan da ke kasa za su caji masu karɓar bashi, walau kamfanoni, ko gwamnatoci, ko ɗaiɗaikun mutane da ke hada-hadar kudi a kasar.
Babbar manufar ƙayyade kudin ruwa ita ce sarrafa yawan kudade da ke hannun mutane. Ana kokarin rage yawan kudi da ke yawo a tattalin ariziki don shawo kan hauhawar farashi, ko kuma a kara yawansa don habaka cinikayya da hada-hadar kudi a tattalin arziki.
A zaman kwamitin da Mista Cardoso ya jagoranta, an kuma kara mafi ƙarancin adadin tsabar kudin da ake bukatar bankunan kasuwanci su ajiye a lalitarsu zuwa kashi 45 cikin 100, na kason jimillar adadin kudaden ajiya da kwastomomin bankin suka zuba a asusun kowane banki.
Haka kuma, an bar adadin ƙarfin iya biyan bashi da bankuna ke da shi a kashi 30 cikin 100, wanda adadi ne da ake aunawa da yawan tsabar kudi da bankuna ke da shi idan an kwatanta da bashin da ake bin su.