Babban Bankin Nijeriya CBN ya ce za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi a ƙasar, a yayin da wa'adin daina amfani da su da aka saka tun farko ke cika a watan gobe.
Sanarwar ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden ta kawo karshen rashin tabbas na tsawon watanni da aka shiga, bayan da yunkurin daina amfani da su a farkon wannan shekarar ya haifar da karancin kudi a Nijeriya.
A ranar Talata, CBN ya ce "za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin a matsayin doka, har bayan wa'adin farko na daina amfani da su da aka saka na ranar 31 ga watan Disamban 2023".
"Babban Bankin Nijeriya na aiki tare da hukumomin da abin ya shafa don janye hukuncin kotun da ke kan wannan batu," in ji sanarwar da CBN ya wallafa a shafin X.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Bankin Isa AbdulMumin ya fitar, ya ce CBN zai ci gaba da fitar da karbar duk takardun kudin, daga tsofaffi har wadanda aka sauya, wajen duk wata hada-hada a bankuna da tsakanin mutane.
“Ana umurtar jama’a da su ci gaba da karbar duk takardun kudin Naira (tsofaffi ko kuma wanda aka sauyawa fasali) don yin mu’amalar yau da kullum, sannan kuma su dinga matukar kulawa tare da wadannan takardun kudi, don kiyayewa da kuma kare darajar kudaden,” in ji sanarwar.
A watan Maris ne dai Kotun Ƙolin Nijeriya ta umarci CBN da ya tsawaita lokacin amfani da tsofaffin kudade na takardun Naira 1,000 da 500 da 200, wadanda janye su da aka yi daga watsuwa ya zamo wani batu da ya jawo ce-ce-ku-ce a lokacin zaɓe, tare da haifar da wahalhalu da fushi a tsakanin al'umma.
A wancan lokacin, ƙarƙashin mulkin tsohon gwamnan bankin Godwin Emefiele da a yanzu yake fuskantar tuhumar kotu, bankin ya kare matsayarsa ta daina amfani da takardun kudaden, yana mai cewa zai yi wahala a iya yin jabun sababbin da zai buga, sannan kuma tsarin zai taimaka wajen shawo kan matsalar tabarbarewar tattalin arziki, ta yadda ake hada-hada da mafi yawan kudade a wajen bankuna.
A lokacin yakin neman zabe, Shugaba Bola Tinubu ya nuna adawa da dakatar da amfani da tsofaffin takardun kudaden.