Babban Bankin Najeriya CBN ya rusa kwamitocin gudanarwar Bankin Union da Keystone da Polaris.
CBN ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Laraba, yana mai cewa ‘’wannan mataki ya zama dole saboda wadannan bankuna da kwamitocin gudanawarsu sun ki bin ka’idoji da tanadin dokar sashe na 12 (c) da (f) da (g)da ( h) na shekarar 2020 kan bankuna da cibiyoyin kudi.’’
''Laifukan da bankuna suka aikata sun hada da rashin bin ka'idar aiki da gaza gudanar da ayyukan da suka shafi shugabanci da yin watsi da ka'idojin da aka bi wajen ba su lasisi da kuma cusa kai cikin ayyukan da suka haifar da barazana ga harkokin kudi da dai sauransu,'' in ji sanarwar.
Nada sabbin shugabanni
Tuni dai CBN ya fitar da sanarwar nada sabbin shugabannin kwamitocin gudanarwar da za su sa ido tare da gudanar da harkokin da suka shafi bankunan guda uku wato Union da Keystone da kuma Polaris.
An nada Yetunde Oni a matsayin babban daraktar Bankin Union da kuma Mannir Ubali Ringim a matsayin daraktar gudanarwa, sai kuma Hassan Imam a matsayin babban daraktan Bankin Keystone da kuma Chioma A. Mang a matsayin daraktar gudanarwa.
Kazalika an nada Lawal Mudathir Omokayode Akintola a matsayin babban daraktan Bankin Polaris da kuma Chris Oyeka Ofikulu a matsayin daraktan gudanarwa.
Sanarwar ta bukaci sabbin shugabannin su kama aiki nan-take.
CBN ya jaddada samar da tsaro da kare kudaden masu ajiya da kuma ci gaba da jajircewa wajen cika aikinsa na tabbatar da ingantaccen tsarin hada-hadar kudi a Nijeriya.
''Tsarin Bankinmu ya kasance mai karfi da jariya,'' in ji sanarwar CBN.