Ana safarar zinare na biliyoyin daloli daga Afirka a kowace shekara, inda akasari ake tafiya da shi zuwa birnin Dubai na ƙasar Haɗaddiyar Daular Larabawa UAE kafin a sake fitarwa zuwa wasu ƙasashe bisa doka, a cewar wata ƙungiya mai zaman kanta ta ƙasar Switzerland a ranar Alhamis.
Kungiyar samar da ayyukan ci gaba 'Swissaid' ta wallafa wani rahoto da ke cewa, a duk shekara ana fitar da ton 321 zuwa 474 na zinaren Afirka da ake samarwa ta ƙananan hanyoyin haƙar ma'adinai, wadanda darajarsu ya kai tsakanin dala biliyan 24 zuwa 35.
Afirka ita ce babbar nahiyar da ke samar da zinare a duniya, inda ƙasashen Ghana da Afirka ta Kudu da Mali da Burkina Faso ke kan gaba a shekarar 2022.
A cewar ƙungiyar, fasa-kwaurin zinaren Afirka na ɗaɗa karuwa, inda a yanzu adadin ya ''ninka fiye da ninki biyu tsakanin shekarar 2012 zuwa 2022.''
Cibiyar kasuwanci a Dubai
Kungiyar ta ce karfen mai daraja ya kasance "tushen samun kuɗaɗen shiga ga miliyoyin masu aikin hakar ma'adinai da kuma gwamnatoci da dama, sannan hanya ce ta samun kuɗin shiga ga 'yan ta'adda tare da haddasa munanan ayyukan taƙe hakkin bil'adama da lalata muhalli.''
Rahoton ya ware birnin Dubai a matsayin cibiyar kasuwanci ta zinare a duniya, inda daga nan ake fita da shi zuwa ƙasashe waje ciki har da Switzerland.
Ƙungiyar mai zaman kanta ta ƙiyasta cewa a shekarar 2022, ''kashi 66.5 cikin 100 (ton 405) na zinaren da aka shigo da su ƙasar UAE an yi safarar su ne daga ƙasashen Afirka.''
Ta jirgin sama ake tafiya da su zuwa Dubai, "ana sanya su a cikin jakar hannu ko a ba da su ajiya a jiragen ƙasuwa da aka tsara tafiya a ciki ko dai ta jirage masu zaman kansu.''
Masana'antun sarrafa zinare
Masarautar tana da masana'antun sarrafa zinare da kuma dubban ‘yan kasuwan ƙarafa da duwatsu masu daraja.
Daga can, musamman ake aika zinaren na Afirka zuwa Switzerland, ''ƙasa ta biyu mafi girma da take shigar da kayan'' sai kuma Indiya.
A karkashin dokar Switzerland, wuri na karshe da ake sarrafa zinaren shi ne inda aka samo shi, don haka duk zinaren da ya isa Switzerland ba daga Afirka aka samo shi ba, in ji kungiyar.
Rahoton ya kunshi bayanai tsakanin shekarar 2012 zuwa 2022 wadanda aka tattaro daga ƙasashen Afirka 54, inda suka yi nuni kan bayanan samar da zinare da kuma kayayyakin da ake shiga da fita da su a hukumance.