Sojojin sun kashe jariri ɗan wata bakwai mai suna Sam Fahd Abu Haikal, tare da jikkata iyayensa, duk da rahotanni sun tabbatar motar ta tsaya a lokacin da aka ba da umarnin tsayawa.
Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin cewa sun harbi motar ne bayan sun yi zaton motar tana tunkararsu, yayin da bincike na wucin-gadi ya nuna cewa waɗanda abin ya shafa fararen-hula ne da ba su da alaƙa da wani rikici.
