'Yan Houthi sun kaddamar da makamai masu linzami kan Isra'ila
Wasu bidiyoyi da Cibiyar Watsa Labarai ta Ansarullah, wacce ke alaƙa da ƙungiyar Houthi ta fitar, sun nuna yadda aka harba makamai masu linzami da ƙungiyar ta ce an kai hari da su ne kan yankin Jaffa kusa da Tel Aviv, a Isra'ila ranar Litinin.
An saki bidiyoyin ne 'yan sa'o'i bayan Isra'ila ta sanar da kai hare-hare cibiyar sinadarai ta Mahshahr a Iran, inda aka ga hayaƙi mai yawa yana tashi daga yankin.
A ranar Litinin, ita ma Houthi ta sanar da haramta wa jiragen ruwan Isra'ila wucewa ta Bahar Maliya