An dawo da mutanen ne a cikin jirgin saman Air Peace, wanda ya sauka a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas ranar Laraba.
Tun da farko, gwamnati ta gudanar da jigilar dawo da ’yan Nijeriya sau shida ta jiragen sama, inda ta dawo da ɗaruruwan ’yan Nijeriyar daga Afirka ta Kudu sakamakon yadda ake cikin fargaba saboda hare-haren da suka shafi ƙyamar baƙi.
