Ma'aikatan kashe gobara fiye da 200 ne suke aiki tare da agajin sojojin sama, domin kashe gobarar bayan da wani baƙin hayaƙi ya mamaye yankin.
Hakan na faruwa ne a yayin da yanayin zafi yake ci gaba da ƙaruwa a ƙasashen Turai da dama, sakamakon sauyin yanayi, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane fiye da 3,700.
