| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Trump ya ce Amurka za ta bar Iran cikin makonni 2 zuwa 3
Shugaban Amurka ya yi iƙirarin cewa tuni aka fara cim ma burin hana Iran mallakar makamin nukiliya ta hanyar matakin soji.
Trump ya ce Amurka za ta bar Iran cikin makonni 2 zuwa 3
Trump na nuna cewa hare-haren kan Iran sun kusa zuwa ƙarshe. / AP

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dakarun ƙasarsa za su bar yaƙin Iran cikin "makonni biyu zuwa uku," inda yake nuna kawo ƙarshen hare-haren da ake kaiwa ƙasar.

"Abin da zan yi kawai shi ne na bar Iran, kuma za mu yi hakan nan ba da jimawa ba," kamar yadda Trump ya shaida wa manema labarai a Fadar White House.

"Za mu bar wurin nan ba da jimawa ba," in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa hakan zai iya faruwa “cikin makonni biyu ko uku."

Ya ce an riga an cim ma burin gwamnatinsa na hana Iran mallakar makamin nukiliya.

"Ba za su samu makamin nukiliya ba. Kuma an riga an cim ma wannan burin," in ji shi.

Masu AlakaTRT Afrika - Trump ya dakatar da hari kan tashoshin makamashin Iran na kwana 10, ya ce ana 'ci gaba' da tuntuɓa

Trump ya kuma ce hare-haren Amurka sun raunata ikon sojin Iran sosai, yana mai iƙirarin cewa Tehran za ta shafe “shekaru 15 zuwa 20” kafin ta iya sake gina ƙarfin sojinta.

"Za mu bar (ƙasar) nan ba da jimawa ba, kuma idan Faransa ko wasu ƙasashe na son samun mai ko gas, za su bi ta Mashigar ruwan (Hormuz)," in ji shi.

"Za su iya biya wa kansu buƙata. Ina ganin zai kasance wuri mai aminci, amma babu ruwanmu da wannan."

Amurka da Isra’ila sun yi ta kai hare-hare kan Iran tun ranar 28 ga watan Fabrairu, inda suka kashe fiye da mutum 1,340, in ji hukumomin Iran.

Iran ta mayar da martani da hare-haren jirage mara matuƙa da makamai masu linzami kan Isra’ila da Jordan da Iraƙi da ƙasashen Larabawa na gaɓar teku da ke da sansanonin sojin Amurka.

Aƙalla jami’an sojin Amurka 13 ne aka kashe tun lokacin da yaƙin ya ɓarke, in ji bayanai na hukuma.

Rikicin ya tayar da farashin makamashi tare da katse jigilar kayayyaki ta Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar mai ta duniya inda kashi 20 na mai da duniya ke amfani da shi ke wucewa.

Rumbun Labarai
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
Araghchi ya faɗaɗa zirga-zirgar diflomasiyyar Iran daga Islamabad zuwa Moscow
Sisi na Masar ya yi gargaɗi kan 'ƙoƙarin da ake yi da gangan' na sake zana taswirar Gabas ta Tsakiya
Falasɗinawa na kaɗa ƙuri'a a zaɓen farko tun bayan yaƙin ƙare-dangi da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza
Iran ta ce ba kai-tsaye za a yi tattaunawa a Pakistan don kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila ba
Turkiyya da ƙasashe bakwai sun soki Isra'ila kan keta alfarmar Masallacin Ƙudus
Trump ya fasa kai wa Iran hari da makamin nukiliya
Daraktan IEA ya ce ana asarar gangar mai miliyan 13 kullum saboda rufe Mashigar Hormuz
Amurka ta dakatar da jigilar dala zuwa Iraƙi, amma me ya sa take aika kuɗi zuwa Baghdad?
Trump ya tsawaita tsagaita wutar Iran domin bai wa Tehran ƙarin lokaci na tattaunawa
Vance zai tafi Pakistan ranar Talata domin tattaunawa da Iran  — rahoto
Sojan Isra’ila na shan suka bayan ya lalata mutum-mutumin Yesu a Lebanon
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan jiragen Amurka a kan ƙwace jirgin dako: Rahoto
Isra'ilawa da dama sun mamaye Masallacin Ƙudus a ƙarƙashin rakiya da tsaron 'yansanda mai tsanani
Trump ya ce Amurka na yin tattaunawa mai kyau da Iran, ya yi gargaɗi kan rufe Mashigar Hormuz
Hare-haren Iran sun lalata fiye da gidaje 1,000 tare da mayar da su kufai a Tel Aviv - Magajin Gari
Iran ta kama mutum 127 kan zargin taya abokan gaba shirya kai mata hari ta ƙasa
Trump ya ce za a yi amfani da ‘manyan katafilolin tone kasa’ don kwashe sinadarin Uranium daga Iran
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya
Jakadan Iran a MDD ya bayyana ƙawanyar Amurka a matsayin 'matakin tsangwama'