| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Kalin ya karɓi baƙuncin tawagar Hamas don tattauna shirin zaman lafiya na Gaza
Tawagar Hamas ta bayyana godyarta ga Turkiyya bisa kokarin Turkiyya na samar da zaman lafiya a Gaza.
Kalin ya karɓi baƙuncin tawagar Hamas don tattauna shirin zaman lafiya na Gaza
Ibrahim Kalin ya marabci tawagar Hamas a Istanbul don tattauna hanyoyin da za a bi don dorewar tsagaita wuta a Gaza. / AA / AA

A cewar majiyoyin tsaron Turkiyya, shugaban Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) Ibrahim Kalin ya gana da Khalil al-Hayya, shugaban tawagar tattaunawa ta ofishin siyasa na Hamas, da kuma tawagar Hamas da ke tare da shi domin tattauna halin da ake ciki a Gaza.

Taron, wanda aka gudanar a Ankara ranar Talata, ya mayar da hankali kan hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa Gaza da kuma mummunan rikicin jinƙai da ke kara ta'azzara, da kuma tashin hankalin da ya barke a yankin Gabar Yamma da aka mamaye da kuma takunkumin da aka sanya wa Masallacin Al-Aqsa na Kudus.

Jami'ai sun jaddada muhimmancin Isra'ila ta cika wajibcinta a karkashin mataki na farko na shirin zaman lafiya na Gaza tare da yin bitar matakan da ake bukata don ci gaba da mataki na biyu.

Tawagar Hamas ta nuna godiya ga kokarin Turkiyya na inganta zaman lafiya a Gaza, suna mika godiya ga Shugaba Recep Tayyip Erdogan saboda ci gaba da hadin gwiwar Ankara kan batun.

Tawagar Hamas ta kuma yi taro da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan.

Rumbun Labarai
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
Araghchi ya faɗaɗa zirga-zirgar diflomasiyyar Iran daga Islamabad zuwa Moscow
Sisi na Masar ya yi gargaɗi kan 'ƙoƙarin da ake yi da gangan' na sake zana taswirar Gabas ta Tsakiya
Falasɗinawa na kaɗa ƙuri'a a zaɓen farko tun bayan yaƙin ƙare-dangi da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza
Iran ta ce ba kai-tsaye za a yi tattaunawa a Pakistan don kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila ba
Turkiyya da ƙasashe bakwai sun soki Isra'ila kan keta alfarmar Masallacin Ƙudus
Trump ya fasa kai wa Iran hari da makamin nukiliya
Daraktan IEA ya ce ana asarar gangar mai miliyan 13 kullum saboda rufe Mashigar Hormuz
Amurka ta dakatar da jigilar dala zuwa Iraƙi, amma me ya sa take aika kuɗi zuwa Baghdad?
Trump ya tsawaita tsagaita wutar Iran domin bai wa Tehran ƙarin lokaci na tattaunawa
Vance zai tafi Pakistan ranar Talata domin tattaunawa da Iran  — rahoto
Sojan Isra’ila na shan suka bayan ya lalata mutum-mutumin Yesu a Lebanon
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan jiragen Amurka a kan ƙwace jirgin dako: Rahoto
Isra'ilawa da dama sun mamaye Masallacin Ƙudus a ƙarƙashin rakiya da tsaron 'yansanda mai tsanani
Trump ya ce Amurka na yin tattaunawa mai kyau da Iran, ya yi gargaɗi kan rufe Mashigar Hormuz
Hare-haren Iran sun lalata fiye da gidaje 1,000 tare da mayar da su kufai a Tel Aviv - Magajin Gari
Iran ta kama mutum 127 kan zargin taya abokan gaba shirya kai mata hari ta ƙasa
Trump ya ce za a yi amfani da ‘manyan katafilolin tone kasa’ don kwashe sinadarin Uranium daga Iran
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya
Jakadan Iran a MDD ya bayyana ƙawanyar Amurka a matsayin 'matakin tsangwama'