Iran ta bayyana cewa ba tsagaita wuta take nema ba, tana neman a kawo ƙarshen yaƙi ne a faɗin yankin.
Kafafen yaɗa labaran Amurka da dama sun bayar da rahoton cewa, ministocin harkokin wajen ƙasashen Masar, Turkiyya, da Pakistan suna ƙoƙarin ganin an gudanar da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a ranar Lahadi.
Jaridun Wall Street Journal da Axios sun ruwaito cewa, ministocin harkokin wajen ƙasashen uku sun tattauna ta wayar tarho karo daban-daban da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, da kuma manzon musamman na Shugaban Amurka Donald Trump, Steve Witkoff, a ƙarshen mako, sai dai ba a samu wani gagarumin ci gaba ba.
Shafin Axios ya ambato wasu majiyoyi biyu da ke da masaniya kan tattaunawar, waɗanda suka bayyana cewa ana gudanar da tattaunawar ce ta hannun masu shiga tsakani daga Pakistan, Masar, da Turkiyya, sannan kuma ana aika saƙonnin tes tsakanin masu bai wa Trump shawara da Araghchi.
Tun da fari, Araghchi ya bayyana cewa tuntuɓar da ake yi da Amurka ba tattaunawar sulhu ba ce, kawai dai musayar saƙonni ce—ko dai kai-tsaye ko kuma ta hannun masu shiga tsakani na yankin.
Tsagaita wuta na wucin-gadi
Jami’an Iran sun ki sassauta bukatunsu, inda suka yi watsi da shawarar sake buɗe Mashigar Hormuz domin a tsagaita wuta ta ɗan wani lokaci, kamar yadda jaridar Journal ta ruwaito.

Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana a ranar Talata cewa, Iran ba ta neman tsagaita wuta ba ne, manufarta ita ce a kawo ƙarshen yaƙi baki ɗaya a yankin.
Masu shiga tsakanin suna ƙoƙarin ganin an cimma matsaya kan wasu matakai na ƙarfafa yarda da aminci waɗanda za su iya sa Trump ya ƙara wa’adin da ya bayar, domin samar da damar gudanar da tattaunawa ta fuska-da-fuska.
Trump ya sanya wa’adin yammacin ranar Talata agogon Amurka a matsayin ranar ƙarshe, inda ya yi gargaɗin cewa Iran za ta rasa kowace tashar samar da wutar lantarki da manyan gine-ginen ƙasar idan har aka ci gaba da rufe mashigar ruwan.
Tun daga ranar 28 ga watan Fabrairu, Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran hari, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 1,340, ciki har da tsohon jagoran addinin ƙasar, Ali Khamenei. Ita ma Iran ta mayar da martani da hare-hare a faɗin yankin, tare da takaita zirga-zirga a mashigar tekun Hormuz, lamarin da ya dakatar da zirga-zirgar gangar mai kusan miliyan 20 a kullum, tare da haddasa fargaba a kasuwannin duniya.












