| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Sharuɗɗa 10 na zaman lafiya da Amurka ta amince da su a yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran
Majalisar Ƙoli ta tsaron ƙasar Iran ta ce sharuɗɗan za su kasance tsarin da za a fara tattaunawa a kansa ranar Juma'a.
Sharuɗɗa 10 na zaman lafiya da Amurka ta amince da su a yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran
Iran ta ce Amurka ta yi amince da muhimman sharruɗan tattaunawa na kjawo ƙrshen rikicin [Tsohon hoto] / Reuters / Reuters
13 awanni baya

Iran ta ce Amurka ta yi "ƙwarya-ƙwaryar" amincewa da sharuɗɗa 10 na kawo ƙarshen yaƙin, in ji rahotanni da kafar watsa labaran ƙasar (IRIB).

Majalisar ƙolin ta tsaron ƙasar ta bayyana ranar Laraba cewa sharuɗɗan za su kasance tsarin da za a fara tattaunawa a kansa domin cim ma yarjejeniya mai faɗi.

IRIB, wadda ta yi ishara ga sanarwar, ta ce sharuɗɗan sun haɗa da tabbacin daina kai hari na tsangwama da ci-gaban Iran da tabbatar da ikonta na gudanar da Mashigar ruwan Hormuz da kuma amincewa da ‘yancin Tehran na sarrafa yuraniyom.

Kazalika Iran ta buƙaci a janye dukkan takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa ƙasar da soke ƙudurorin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) da kuma hukumar nukiliya ta IAEA ta ƙaƙaba wa Iran, da biyan diyya da kuma janye dakarun Amurka daga yankin.

Tsarin tattaunawa

Majalisar ta jaddada cewa duk wata yarjejeniya da za a yi daga baya za ta dogara ne kan cika sharuɗɗan Iran da kuma tabbatar da yarjejeniya kan bayanan cikinta ɗaya bayan ɗaya.

A nata ɓangaren, Iran ta ce za ta bari jiragen ruwa su ci gaba da wucewa ta Mashigar ruwan Hormuz cikin aminci yayin tattaunawar.

An saka ranar Juma’a a matsayin ranar da za a fara tattaunawa a birnin Islamabad a ƙarƙashin shiga tsakanin Pakistan kuma ana sa ran za a shafe makonni biyu ana yinta.

Masu AlakaTRT Afrika - Mazauna Tehran sun fada halin rashin tabbas bayan barazanar Trump ta baya bayan nan

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana daga farko cewa Washington za ta dakatar da hare-hare kan Iran tsawon makonni biyun, inda ya bayyana sharuɗɗan Tehran a matsayin “tushen da za iya” tattaunawa a kai.

Kafofin watsa labaran Iran sun ce, takardar sharuɗɗan sun nemi a janye takunkuman Amurka na matakin farko da na mataki na biyu da kuma janye ƙudurorin MDD da ma na hukumar makamashin nukiliya ta duniya a kan Iran tare da biyan diyya.

Tsarin ya kuma nemi janye dakarun yaƙin Amurka daga yankin da kuma kawo ƙarshen hare-hare a duk wurare, ciki har da Lebanon.

Ƙarin bayanai da kafofin watsa labaran Iran suka ruwaito sun nuna cewa tsarin ya bayyana hanya mai faɗi ta kawo ƙarshen yaƙin.

Jaridar The New York Times ta ba da rahoton cewa shirin, wanda aka tura Amurka ta hannun masu shiga tsakani na Pakistan, na neman sasantawa ta dindindin da kuma wata hanya ta biyan diyya domin kawo ƙarshen rikicin.

Idan aka buɗe Mashigar ruwan Hormuz domin jigilar kayayyaki, za a raba kuɗin wucewa da ya kai dala miliyan 2 kan ko wane jirgin ruwa tsakanin Iran da Oman, in ji Iran.

Maimakon a biyan diyya kai-tsaye, Iran za ta yi amfani da kuɗin shigewar domin sake gina ababen more rayuwarta da aka lalata yayin hare-haren Amurka da Isra’ila.