Mojtaba Khamenei, malamin da aka daɗe ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin mafiya ƙarfin faɗa-a-ji wanda ba kasafai ake ganinsa ba a cikin jagororin siyarsar Iran, ya zama sabon jagoran addinin ƙasar bayan kisan da aka yi wa mahaifinsa a wani harin Amurka da Isra’ila.
Majalisar ƙwararru ta Iran, wadda ta ƙunshi mutum 88 kuma take da alhakin naɗa manyan jami’an addini da na siyasar ƙasar bisa kundin tsarin mulkin ƙasar, ce ta zaɓi malamin mai shekara 56.
Da naɗinsa, Mojtaba ya zama jagoran addinin Iran na uku tun juyin juya halin shekarar 1979, inda ya zama shugaba a wani mawuyacin lokaci na yankin Gabas ta Tsakiya da kuma rashin tabbas a cikin ƙasar.
Farkon rayuwa da irin gidan da ya fito
An haifi Mojtaba ranar 8 ga watan Satumba, shekarar 1969, a birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin karantarwa ta addini a ƙasar.
Ɗa na biyu ne ga Ali Khamenei, wanda ya yi mulki a matsayin jagoran addini daga shekarar 1989 zuwa lokacin da aka kashe shi a fiye da mako ɗaya da ya gabata a hare-haren saman Amurka da Isra’ila, tare da jikan malamin Javad Khamenei.
Da yake tasowa a cikin wani yanayi mai tashin hankali na siyasa, Mojtaba ya shaida yadda mahafinsa ya yi ƙarfi a matsayin muhimmin mutum a ƙasar kuma daga baya ya zama shugaban ƙasar Iran kafin ya kama aiki a matsayin jagoran addini.
Ya auri Zahra Haddad-Adel, ‘ya ga Gholam-Ali Haddad-Adel, wani fitaccen ɗan siyasa mai ra’ayin ‘yan mazan jiya kuma tsohon shugaban majalisar dokoki wanda a halin yanzu yana jagorantar ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin al’adun Iran.
Zahra na cikin waɗanda aka kashe a harin Amurka da Isra’ila wanda ya afka wa harabar gidan iyalan Khamenei a babban birnin ƙasar, Tehran. Mojtaba ya tsira daga harin, amma ya rasa mahaifiyarsa da ‘yar’uwarsa da mijin ‘yar’uwarsa da kuma ‘ya’yan ‘yan’uwansa.
Karatu da kuma horaswa na malanta
Kamar da yawa daga cikin malamai masu iko a Iran, Mojtaba ya yi karatunsa na addini a birnin Qom, cibiyar karatun addini mafi shahara a ƙasar.
Masu sharhi kan Iran sun ce Mojtaba ya shafe da yawa daga cikin shekarun aikinsa yana koyarwa a makarantun na Qom, ciki har da karantar da fiƙihu mai zurfi da aka fi sani da dars-e kharej, wanda ake ganin shi ne mataki mafi girma na karatun addini.
Mojtaba bai taɓa neman muƙamin siyasa ba ko kuma a saka shi a zaɓen da jama’a za su ƙada ƙuri’u, amma ya shafe gomman shekaru a matsayin wani mutum mai tasiri sosai a cikin makusanta tsohon jagoran addinin ƙasar, inda ya ƙulla alaƙa mai zurfi da Rundunar Kare Juyin Juya Halin Iran (IRGC).
Rawar da yake takawa da kuma tasirinsa
Kafofin watsa labaran ƙasashen waje suna yawan bayyana Khamenei a matsayin wani mutum da ba za a iya gane masa ba wanda mai yiwuwa yana da tasiri a bayan fage.
Rashin yawan ganinsa a bainar jama’a ya sake ƙarfafa wannan tunanin, saboda babu jawabai ko hirarraki masu yawa a kansa.
Daga lokaci zuwa lokaci sunan Mojtaba na fitowa a tattaunawar siyasa a Iran, yawanci idan ana maganar zaɓen shugaban ƙasa ko kuma hasashe game da wane ɗantakara zai goya wa baya.
Duk da haka Mojtaba da kansa ba ya yawan shiga muhawarar siyasa a fili. Fitowarsa dai ta taƙaita ne kan bukukuwa na hukuma da bukukuwan tunawa na ƙasa da kuma tarukan addini da kafofin watsa labarai mallakar ƙasar Iran suke ɗauka.
Lokaci na baya da aka gan shi a fili shi ne yayin wani jerin gwanon goyon bayan gwamnati bayan zanga-zanga da aka yi a wurare da dama a farkon wannan shekarar.
Rahotanni daga ƙasar Iran sun ce Mojtaba ya taka rawa a yaƙin Iraƙi da Iran da aka yi a shekarun 1980 lokacin da mahaifinsa ke aiki a matsayin shugaban ƙasa.
Rahotanni sun ce ya shiga cikin ‘yan sa-kai a matsayinsa na matashi, lamarin da ya ba shi damar taka rawa a karon farko a fagen daga.
Gado na fuskantar barazana
Mojtaba Khamenei zai karɓi ragamar ƙasar ne a ɗaya daga cikin lokuta mafiya rashin tabbas a tarihin Iran na baya bayan nan.
Sauya shugabancin na kuma faruwa ne a yayin da ƙasar ke fuskantar barazana kai-tsaye daga Ira’ila, wadda shugabanninta suka sha alwashin kashe duka wani shugaba da aka zaɓa domin ya gaji Ali Khamenei.
"Duk wani shugaba da gwamnatin ta’addancin Iran ta zaɓa domin ci gaba da jagorantar shirin lalata Isra’ila da barazana ga Amurka da duniyar ‘yanci da kuma ƙasashe a yankin tare da danne mutanen Iran, zai kasance wanda za a kashe, ko mene ne sunansa ko kuma ina yake ɓuya," kamar yadda ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya bayyan a shafinsa na X.
Barazanar na nuna irin matsanancin matsin da ke zagaye da maye gurbin jagoran, lamarin da ya sa Mojtaba a tsakiyar arangama ta yanki wadda ta zarta kan iyakokin Iran.
Ma’aikatar baitul malin Amurka ta ƙaƙaba wa Mojtaba takunkumi a shekarar 2019, tana mai cewa yana wakiltar jagoran addini a "wani mataki na hukuma duk da cewa ba a taɓa zaɓensa ko kuma naɗa shi wani muƙamin gwamnati ba " baya ga aiki a ofishin mahaifinsa.













