Bayan shafe awanni ana tattaunawa, Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta kammala Babban Taron Ƙasa na 8, inda aka sake zaɓen Nentawe Yilwatda a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Baya ga Yilwatda, jam’iyyar mai mulki ta zaɓi Surajudeen Basiru a matsayin sakatare. Su biyun tare da sauran mambobin Kwamitin Ayyuka na Ƙasa NWC an zaɓe su ne ta hanyar yarjejeniya wadda wakilai suka amince da ita a wajen taron.
Kwamitin Zaɓen Taron ya sanar da sunayen mambobin kwamitin ayyukan a lokacin Babban Taron Zaɓe na Ƙasa na huɗu na APC.
Sauran waɗanda suka samu muƙaman sun haɗa da Felix Morka a matsayin sakataren yaɗa labarai, da Dayo Israel wanda ya ci gaba da riƙe mukaminsa na jagoran matasa.
Yilwatda ya ce sake zaɓensa kira ne na yin hidima, yana mai nuna godiyarsa ga APC bisa damar da aka ba shi.
Ya ce, “Mun shirya mu yi aiki, mun shirya mu yi jagoranci, kuma mun shirya mu gina jam’iyyar tare da ƙasa, tare da ku,” a yayin jawabin da ya yi bayan samun nasara.
Ya kuma yi alƙawarin cewa kwamitin ba zai “gaza ko ja da baya ba” wajen aiwatar da ayyukanta.
Taron, wanda aka gudanar a dandalin Eagle Square a Abuja, ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, mataimakinsa Kashim Shettima, shugabanni da ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa, gwamnoni na APC da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
A wajen taron da ya samu halartar wakilai fiye da 8,000, Tinubu ya shaida wa mahalarta cewa ƙasar na kan turba mai kyau.
Ya ce duk da cewa hanyar tana da ƙalubale, gyare-gyaren da gwamnatinsa ta fara aiwatarwa matakai ne da suka zama dole domin daidaita hanyar ci gaban Nijeriya.
Ya ce, “Mun san sake gina Nijeriya na buƙatar jarumtaka, haƙuri da ɗaukar matakai masu wahala. Amma mun kuma san cewa babu wata ƙasa da ke ci gaba ta hanyar guje wa gaskiya.”
Sai dai tsohon gwamnan Jihar Legas ɗin ya ƙara da cewa, “muna kan hanya mai kyau. Amincewar masu zuba jari ta ƙaru matuƙa.”
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, duk da yawan katsewar wutar lantarki, akwai nasara na nan tafe a nan g







