| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutane tara, wasu da dama sun ɓata a gaɓar tekun Djibouti
Hatsarin jirgin ruwan ya afku a daren 24 ga Maris a gaɓar tekun Djibouti, in ji hukumar gudun hijira ta Majalisa Dinkin Duniya.
Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutane tara, wasu da dama sun ɓata a gaɓar tekun Djibouti
Jirgin ruwan ya kife a gabar tekun Djibouti, arewa da Obock. / Reuters
11 awanni baya

‘Yan gudun hijira tara ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 45 suka ɓata sakamakon karyewar jirgin ruwan da suke ciki a gaɓar tekun Djibouti a makon nan, in ji hukumar gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IMO) a ranar Alhamis.

Dubban ‘yan gudun hijira na amfani da ‘Hanyar Gabas’ da ke Kusurwar Afirka zuwa ƙasashen Larabawa a kowace shekara don neman ayyukan yi ko aikatau a gidaje a kasashen yanki Tekun Fasha.

A bara an samu mutuwar mutane 922 wanda ya ninka na shekarar 2024, a cewar Hukumar Gudun Hijira ta Kasa da Kasa.

“Mummunan hatsarin jirgin ruwan ya afku a daren 24 ga Maris a gaɓar tekun Djibouti, arewa da Obock. Mutane 9 sun mutu, wasu 45 sun bata, daga cikin fasinjoji 320 da ke cikin jirgin,” in ji IMO ta shafin X.

Mafi yawan ‘yan gudun hijirar sun fito ne daga ƙasar Ethiopia kuma suna tsallakawa ta Djibouti zuwa Yemen.