| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin ruwan Nijeriya sun kama masu tserewa Turai a ɓoye ta jirgin ruwa a Legas
Mutanen da ake zargi da aikata laifin an kama su ne suna ɓoye a cikin wani ɓangare na ƙasa a bayan jirgin ruwan mai suna MV Seaspan Lahore yayin wani bincike na yau da kullum da jami’an sojin ruwan ke yi.
Sojojin ruwan Nijeriya sun kama masu tserewa Turai a ɓoye ta jirgin ruwa a Legas
Hafsan sojin ruwan ya bayyana cewa tafiya a jirgin ruwa a ɓoye na da haɗari baya ga saɓa wa doka / Reuters
2 awanni baya

Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta kama mutum biyu masu neman tserewa Turai ɓoye a jirgin ruwa a tashar jiragen ruwan Legas.

Mutanen da ake zargi da aikata laifin an kama su ne suna ɓoye a cikin wani ɓangare na ƙasa a bayan jirgin ruwan mai suna MV Seaspan Lahore yayin wani bincike na yau da kullum da jami’an sojin ruwan ke yi.

An bayyana cewa sunayensu Abdullahi Yakubu, mai shekara 36 da  Omoniyi Afotona, mai shekara 25.

An miƙa mutanen biyu ga jami’an hukumar shige da ficen Nijeriya da ke sa ido kan tashoshin jiragen ruwa da hanyoyin ruwa a Apapa, domin ƙarin bincike da kuma yiwuwar gurfanar da su a gaban kotu.

Da yake magana a wajen miƙa su, kwamandan rundunan sojin ruwan ƙasar ta NNS BEECROFT, Commodore A. Adams-Aliyu, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne da sanyin safiyar ranar Alhamis 19 ga watan Maris na shekarar 2026, yayin da jirgin ke shirin tafiya a Legas.

Ya bayyana cewa mai irin wannan laifin shi ne mutumin da ya shiga jirgin ruwa domin tafiya a ɓoye ba bisa ƙa’ida ba.

Adams-Aliyu ya yi gargaɗin cewa tafiya a jirgi a ɓoye ta saɓa wa doka kuma tana da haɗari, yana mai kira ga iyaye su ilimantar da matasa game da haɗarin irin wannan tafiya.

Ya bai wa ‘yan Nijeriya masu neman damar-damarki a ƙasashen waje fita ta hanyoyin da suka dace.