| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Gobara ta tashi bayan Iran ta kai harin jirage marasa matuƙa kan matatar mai a Kuwait
Iran ta kai hari da da jirage marasa matuƙa kan matatar mai ta Kuwait a yayin da Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a Tehran, abin da ya ƙara dagula lamura a Gabas ta Tsakiya da kuma ƙara fargaba a fannin makamashi na duniya.
Gobara ta tashi bayan Iran ta kai harin jirage marasa matuƙa kan matatar mai a Kuwait
Wata tanka tana ɗaukar mai a Gaɓar Mina Al AHmadi, mai nisan mil 25 (40 km) da ke kudancin Kwait City a wannan hoton da aka ɗauka a Yulin 2008. / AP
9 awanni baya

Iran ta kai hari da jirage marasa matuƙa kan matatar mai ta Kuwait ranar Jumma’a sannan jiniya ta yi ta ƙara a Isra’ila da ke nuna cewa hare-hare na kan hanya, kana an ji fashewar abubuwa a Tehran a yayin da Isra’ila ta kai hari birnin a yayin da ƙasar ke bikin Sabuwar Shekarar Farsi.

A yayin da yaƙin da ya gogita tattalin arzikin duniya ya shiga mako na uku, Iran ba ta nuna alamar gazawa ba a hare-haren da take kai wa tashoshin makamashi na yankin Gulf, inda Kuwait ta ce Tehran ta kai hari kan matatar mai ta Mina Al-Ahmadi abin da ya haifar da gobara ko da yake jami’an da ke aiki a matatar sun kashe ta.

Matatar man, wadda ke tace gangar ɗanyen mai 730,000 a kowace rana, dama an lalata ta ranar Alhamis a wani hari da Iran ta kai. Tana ɗaya daga cikin matatun mai uku a Kuwait.

Masu AlakaTRT Afrika - Iran na tunanin fara karɓar kuɗi daga jiragen ruwan da ke son wucewa ta Mashigin Hormuz

Iran ta ƙara ƙaimi wurin kai hare-hare a tashoshin makamashi na Ƙasashen Larabawa bayan da Isra’ila ta kai hari kan babban filinta na iskar gas mai suna South Pars ranar Laraba.

Fashewar abubuwa ta girgiza Dubai sannan gobara ta tashi wani wurin ajiye kaya a Bahrain

Fashewar abubuwa ta girgiza Dubai a yayin da na’urorin tsaron sararin samaniyar birnin suka tare makamai masu linzami da sanyin safiyar Jumma’a, a daidai lokacin da ake Idin ƙaramar sallah.

Ministan harkokin cikin gida na Bahrain ya ce gobara ta tashi bayan tarkacen wani makami da aka kakkaɓo sun faɗa wani wurin ajiye kaya, sannan a Saudiyya hukumomi sun ce sun kakkaɓo jirage marasa matuƙa da suka nufi lardin gabashin ƙasar mai arzikin mai.

Sabbin hare-haren na zuwa ne kwana guda bayan Iran ta matsa ƙaimi wajen kai farmaki a tashoshin makamashi na yankin tare da ƙaddamar da jerin hare-hare na makamai masu linzami a cikin Isra’ila bayan ta kai hari kan filin makamashinta na South Pars.