| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
CAF ta ayyana Maroko a matsayin ƙasar da ta lashe Gasar AFCON 2025
Kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafe na CAF, wanda ya ɗauki wannan mataki, ya ce Maroko ta lashe wasan ƙarshe na gasar AFCON da ci 3-0.
CAF ta ayyana Maroko a matsayin ƙasar da ta lashe Gasar AFCON 2025
Kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafe na CAF, wanda ya ɗauki wannan mataki, ya ce Maroko ta lashe wasan ƙarshe na gasar AFCON da ci 3-0. / AP
2 awanni baya

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta ayyana ƙasar Maroko a matsayin ƙasar da ta lashe gasar cin kofin Afirka ta AFCON 2025, wadda kafin wannan hukuncin ƙasar Senegal ce ta lashe ta.

Kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafe na CAF, wanda ya ɗauki wannan mataki, ya ce Maroko ta lashe wasan ƙarshe na gasar AFCON da ci 3-0.

‘Yanwasan Senegal sun fice daga filin wasa na wani lokaci a wani mataki na ƙin amincewa da wani bugun fenaretin da aka bayar a kansu a yayin da ake dab da kammala wasan ƙarshe da aka yi ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2026 a Rabat, babban birnin Maroko.

Ɗanwasan Maroko Brahim Diaz, wanda aka kayar, ya ɓarar da fenaretin, lamarin da ya kai wasan zuwa ƙarin lokaci.

Pape Gueye ne ya zura ƙwallon Senegal ɗaya tilo a raga da farkon ƙarin lokacin, lamarin da ya sa Teranga Lions ta Senegal ta lashe gasar AFCON 2025, kofin AFCON na biyu da ta lashe a tarihi, bayan nasararta a kan Masar a shekarar 2021.

Shigar da ƙarar Maroko

Bayan sakamakon wasan ƙarshe da aka yi a Rabat, masu masaukin baƙi, Maroko, sun shigar da ƙara a hukumar CAF, inda suka ce matakin Senegal na ficewa daga filin wasa ya sa wasan ya zo ƙarshe tun lokacin tashi bai yi ba, kuma ya kamata a ce an ayyana Maroko a matsayin ƙasar da ta lashe gasar tun wancan lokacin.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, CAF ta amince da ƙarar Maroko kuma ta yanke hukuncin cewa: "An ayyana tawagar ƙwallon ƙafa ta Senegal a matsayin wadda ta sha kaye a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka da TotalEnergies ta ɗauki nauyinta (AFCON) 2025, inda aka rubuta sakamakon wasan cewa an tashi da ci 3–0, nasara ga Maroko."

A takardar ƙararsu, Maroko sun yi ishara ga dokoki na 82 da na 84 daga cikin dokokin gasar cin kofin Afirka.

Doka ta 82 ta ce : "Idan, kan ko wane dalili, wata tawaga ta janye daga gasar ko kuma ba ta zo filin wasa ba, ko kuma ta ƙi ta buga wasa ko kuma ta bar filin wasa kafin ƙarshen wasa ba tare da amincewar alƙalin wasa ba, za a ƙaddara cewa tawagar ta sha kaye kuma za a fitar da ita ta daga gasar da ake yi."

Kofin Maroko na biyu a tarihin gasar AFCON

Doka ta 84 kuwa, ta bayyana cewa: "Tawagar da ta saɓa wa tanade-tanaden doka ta 82 za a cire ta ne daga gasar. Wannan tawagar za ta sha kaye da ci 3-0 sai dai idan abokan hamayya sun ci ƙwallaye fiye da haka a lokacin da aka katse wasan, a irin wannan halin za a ƙyale sakamakon wasan yadda yake."

A hukuncin da ta yanke, CAF ta ce: "majalisar ɗaukaka ƙara ta hukumar CAF ta gano cewa ɗabi’ar tawagar Senegal ta karya dokoki na 82 da na 84 na dokokin gasar cin kofin Afirka. An ɗabbaka ƙarar da Maroko ta shigar . (Saboda haka), an ayyana tawagar a matsayin wadda ta rasa wasan , inda aka rubuta sakamakon wasan a matsayin ci 3–0, nasara ga Maroko."

Sai dai idan Senegal ba ta ji daɗin hukuncin ba, za ta iya ɗaukaka ƙara a kotun ɗaukaka ƙara ta wasanni (CAS), wadda ita ce kotun ƙoli kuma hukuma mai zaman kanta a kan duk saɓanin wasanni, ciki har da hukunce-hukunce kan gasa irin na rasa wasa ko kuma cancanta.

Nasarar Maroko da hukumar CAF ta ayyana yanzu ya bai wa ƙasar kofinta na biyu ta a tarihin gasar AFCON, bayan ta lashe gasar ta shekarar 1976.