| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
China ta yaba wa Turkiyya, Saudiyya, Qatar kan rawa a tsagaita wuta tsakanin Pakistan da Afghanistan
Beijin ta ya kira ga Islamabad da Kabul su 'koma tattaunawar zaman lafiya ba tare da ɓata lokaci ba, su yi aiki don samar da tsagaita wuta gamsasshe mai dorewa' don wanzar da zaman lafiya a yankin.
China ta yaba wa Turkiyya, Saudiyya, Qatar kan rawa a tsagaita wuta tsakanin Pakistan da Afghanistan
Sojojin Taliban suna tsaye a kan wani dogon ginshiƙi, suna gadin kusa da iyakar Pakistan da Afghanistan, a lardin Khost, Afghanistan. / Reuters
19 Maris 2026

A ranar Alhamis, China ta yaba wa rawar da Turkiyya, da Saudiyya da Qatar suka taka wajen cim ma tsagaita wuta tsakanin Pakistan da Afghanistan.

Yayin da ta yi maraba da sanarwar tsagaita wutar da Islamabad da Kabul suka yi, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ta China, Lin Jian, ya ce Beijing na fatan cewa ƙasashen biyu "za su zauna cikin natsuwa, su taka-tsantsan, su koma tattaunawar zaman lafiya ba tare da ɓata lokaci ba, su tabbatar da cikakken dawwamammen tsagaita wuta cikin kankanin lokaci, su magance bambance-bambancen da ke tsakannsu da rikice-rikice ta hanyar tattaunawa yadda ya kamata, kuma su yi aiki tare don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin kasashen biyu da yankin."

"China na yabawa kokarin da wasu ƙasashen Musulunci suka taka," in ji Lin, yana nuni da rawar da Ankara, Riyadh da Doha suka taka wajen cim ma tsagaita wutar.

Ya ce China tana shiga tsakani tsakanin ɓangarorin ta hanyoyinta, kuma tana shirye ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka kamata wajen cim ma wannan yunƙuri.

A ranar Laraba Pakistan ta ce ta dakatar da "ayyukan sojojinta" na “ɗan wani lokaci” saboda bukukuwan sallah na Musulmai, bayan buƙatun Turkiyya, da Saudiyya da Qatar.

Dakatarwar ta ɗan wani lokaci

Daga baya, kakakin gwamnatin Afghanistan, Zabihullah Mujahid, ya sanar da dakatar da ayyukan ƙasarsa na yaƙi na ɗan lokaci gabanin idin Ƙaramar Sallah, yana mai danganta hakan ga kyakkyawar niyya da kuma buƙatun Saudiyya, da Turkiyya da Qatar.

Dangantaka tsakanin Afghanistan da Pakistan ta taɓarɓare a 'yan makonnin nan yayin da tashin hankali a kan iyaka ya ƙaru, wanda ya janyo asarar rayuka da lalata dukiya.

Tun ƙarshen Fabrairu, arangama a iyaka ta yi ajalin akalla mutane 107 a ɓangarorin biyu, ciki har da sojoji 13 da fararen hula 5 a Pakistan, yayin da wani soja har yanzu ba a same shi ba.

Hukumomin Afghanistan sun bayar da rahoton cewa sojoji 13 da fararen hula 76 sun mutu a Afghanistan, ba tare da lissafa sabbin asarar rayuka daga harin da aka kai wani asibitin ba a ranar Litinin, inda jami'an Afghanistan ke iƙirarin cewa harin sama na Pakistan ya kashe mutane 408.

Ofishin da ke taimaka wa Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan ya ba da rahoton mutuwar fararen hula 76 da raunuka 213 a Afghanistan tsakanin 26 Fabrairu da 16 Maris, ba tare da haɗawa da harin na ranar Litinin ba.

Islamabad na zargin Afghanistan da bai wa ƙungiyoyin 'yanta'adda masu adawa da Pakistan mafaka, abin da Kabul ke musantawa.

Rumbun Labarai
An daƙile makami mai linzami na Iran a kan hanyarsa ta kutsawa Turkiyya
Turkiyya ta tura jiragen yaƙi na F-16 shida Arewacin Cyprus yayin yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran
Turkiyya ta kira jakadan Iran, ta nuna damuwarta kan harba makami mai linzami a sararin samaniyarta
NATO ta kakkaɓo makami mai linzami na Iran da aka harba Turkiyya
Shugaba Erdogan ya koka da rushewar tsarin tafiyar da duniya da ke aiki bisa doron dokoki
Hari kan Iran “zalunci ne kuma ba bisa ka’ida ba”, in ji jam’iyya mai mulkin Türkiyya
Shugaba Erdogan ya yi kira kan a yi amfani da diflomasiyya yayin da rikicin Iran ke rincaɓewa
Turkiyya ta yi kira ga Amurka, Isra'ila da Iran su tsagaita wuta nan-take
Ankara ta samar da shafin intanet kan taron COP31 na sauyin yanayi da za a gudanar a Turkiyya
Pakistan da Turkiyya sun yi alƙawarin zurfafa alaƙar tsaro a ziyarar manyan jami'ai zuwa Ankara
Shugaba Erdogan ya miƙa saƙon 'Barka da Azumi' ga ƙasarsa da duniyar Musulmai
Erdogan: Amincewar da Isra'ila ta yi wa Somaliland ba za ta amfani kowa ba
Amurka da Iran na nuna sassauci kan yarjejeniyar Nukiliya: In ji Fidan na Turkiyya
Shugaban Turkiyya ya naɗa sabon Ministan Shari'a da na Harkokin Cikin Gida
Turkiyya tana karɓar baƙuncin taron tattaunawa kan alaƙarta da Ƙasashen Afirka
Adadin jama'ar Turkiyya ya kai miliyan 86 a 2025 yayin da jama'ar ƙasar ke ƙara yawa
Matar Shugaban Turkiyya da Sarauniyar Jordan sun ƙara jaddada ƙawance a Istanbul
Turkiyya ta kama jami'an Mossad na Isra'ila biyu a Istanbul kan leƙen asiri
Shugaba Erdogan ya tuna da girgizar ƙasa, ya ce ‘Turkiyya ta cika alkawarinta‘ na sake gina gidaje
Turkiyya ta bunƙasa taimakon da ta ke ba Somaliya na sojojin sama da ƙasa don yaƙi da ta'addanci