| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Iran ta yi ruwan makamai masu linzami a cikin Isra'ila
Rundunar juyin juya hali ta Iran IRGC ta ce ta kai hare-haren ne a tsakiya da kudancin Isra'ila, ciki har da Tel Aviv da sansanonin sojin Amurka da ke yankin, inda ta ƙara da cewa dukkan hare-haren sun “samu cikakkiyar nasara.”
Iran ta yi ruwan makamai masu linzami a cikin Isra'ila
Iran ta ƙaddamar da jerin hare-hare na makamai masu linzami karo na biyar a cikin Isra’ila / Reuters
20 Maris 2026

Iran ta ƙaddamar da jerin hare-hare na makamai masu linzami karo na biyar a cikin Isra’ila, a cewar kamfanin dillancin labaran Tasnim News Agency na ƙasar Iran.

An ji ƙarar jiniya a Birnin Ƙudus, Galilee da Haifa, kamar yadda kafar watsa labarai ta Channel 12 ta Isra’ila ta ruwaito.

Rundunar juyin juya hali ta Iran Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta ce ta kai hare-hare ne a tsakiya da kudancin Isra’ila ciki har da Tel Aviv da sansanonin sojin Amurka da ke yankin inda ta ƙara da cewa dukkan hare-haren sun “samu cikakkiyar nasara, in ji Tasnim.

Rundunar IRGC ta ƙara da cewa yanzu haka tana ci gaba da kai hare-hare da manyan makamai masu linzami da kuma makamai masu cin gajeren zango.

Masu AlakaTRT Afrika - Iran na tunanin fara karɓar kuɗi daga jiragen ruwan da ke son wucewa ta Mashigin Hormuz

Kafar watsa labarai ta Channel 12 ta ruwaito cewa tarkacen makamai masu linzami sun faɗa cikin Haifa Bay da birnin Shfar'am na arewacin Isra’ila.

Jaridar Yedioth Ahronoth da ke Isra’ila ta ruwaito cewa Iran ta harba makamai masu linzami masu ‘ya’ya cikin Isra’ila awa ɗaya da ta wuce.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra’ila, Magen David Adom, ya ce ba a samu rahoton mutuwa ba daga Haifa kuma babu wata babbar ɓarna da ta faru a Birnin Kudus da kewayensa.

Ya ƙara da cewa an tura tawagar domin kula da mutanen da suka jikkata sakamakon ruɗanin da suka shiga.

MAJIYA:AA
Rumbun Labarai
Isra'ila ta yi asarar $57bn a tattalin arzikinta cikin shekara biyu kan kisan kiyashin Gaza
Sojojin Isra'ila sun azabtar da yaro ɗan shekara ɗaya don tilasta wa mahaifinsa amsa tambayoyi
Ƙasashen Larabawa da ke gaɓar teku sun nuna goyon baya ga Turkiyya, Qatar bayan hatsarin helikwafta
Iran ta ce ‘a buɗe’ Mashigar Hormuz take, amma jiragen ruwa na tsoron wucewa
Gobara ta tashi bayan Iran ta kai harin jirage marasa matuƙa kan matatar mai a Kuwait
Iran na tunanin fara karɓar kuɗi daga jiragen ruwan da ke son wucewa ta Mashigin Hormuz
Shugabannin Turkiyya da Oman sun tattauna kan tashe-tashen hankula da ke ƙamari yayin yaƙin Iran
Amurka ba ta da masaniya kan harin da Isra’ila ta kai filin iskar gas na South Pars a Iran - Trump
Ali Larijani: ‘Gwarzon Wannan Lokaci’ wanda ya haɗa tsoffin jini da sabbin jinin Iran
Isra'ila ta yi ikirarin kashe Sakataren Majalisar Ƙoli ta Tsaron Iran Ali Larijani
Gobara a jirgin Amurka na dakon jiragen yaƙi ta sa matuƙa jirage 600 sun rasa gadaje a yaƙin Iran
Iran ta kai hari kan maƙwabtanta a gaɓar teku, ta ƙara daƙile jigilar mai yayin da fargaba ke ƙaruwa
Iran ta kama mutum 500 kan tuhumar leƙen asiri tun farkon yaƙinta da Amurka da Isra'ila: Jami'i
Iran ta ba da shawarar yin bincike kan hare-hare, ta ce inda ake nufa suna da alaƙa da Amurka
Ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu ta buƙaci Iran ta guji kai hari kan ƙasashe maƙwabta
Trump ya yi ikirarin Amurka ta kai babban harin bam a Tsibirin Kharg na Iran
Wani jirgin sojin Amurka ya faɗi a yammacin Iraƙi
Yaƙin Gabas ta Tsakiya ya haifar da tsaiko mafi girma a tarihi a wurin samar da man fetur
Farashin gangar ɗanyen mai ya ɗara $100 yayin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ke ƙamari
Daga Tashin Kiyama zuwa Amalek: Yadda batutuwan addini ke sake bayyana a yakin Iran