Manchester United ta sanar da cewa ‘yanwasanta na gaba biyu, Bryan Mbeumo da Benjamin Sesko ba za su je waklitar ƙasashensu ba don buga wasannin sada-zumunta.
Mbeumo ɗan Kamaru ne, yayin da Sesko ɗan Slovenia ne, kuma dukkansu ‘yan wasan gaba ne da suke taimaka wa United a tagomashin da take samu a baya-bayan nan.
Sanarwar United ta ce, “Ala tilas Bryan Mbeumo ya fita daga tawagar Kamaru da za ta buga wasan sada zumunta da Australia da kuma China, a matsayin kandagarki, bayan da aka cire shi a minti na 71 a wasan maraicen Juma’a da aka yi canjaras da Bournemouth.
Shi ma Benjamin Sesko ya bar tawagar Slovenia da za ta buga wasan sada zumunta da Hungary da kuma Montenegro, har sai ya samu cikakken sauƙi, cewar sanarwar.
Tun bayan zuwansa daga Brentford, Mbeumo ya ci ƙwallaye 10 a duka gasannin da ya buga. Shi kuwa Benjamin Sesko ya ci ƙwallaye shida a kakar bana tsakanin Janairu da Fabrairu nan.
Sai dai akwai ‘yanwasan da za su bar United don buga wa ƙasarsu, kamar Noussair Mazraoui, wanda zai koma tawagar ƙasarsa Maroko.
A halin yanzu United na mataki na uku a teburin Firimiya a kakar nan ta 2025-26 ƙarƙashin sabon koci, Michael Carrick mai riƙon ƙwarya zuwa ƙarshen kakar bana.
Koci Carrick na fatan ganin Manchester United ta ƙare kakar bana a saman teburi don samun gurbin buga gasar Zakarun Turai a baɗi, kasancewar ba su da wata damar cin kowane kofi a bana.













