Rahotannin daga Napoli ta Italiya na cewa ƙungiyar ta "fusata" kan cewa tauraron ɗanwasanta Romelu Lukaku, ya ƙi komawa yin atisaye a ƙungiyar bayan janyewa daga buga wa ƙasarsa Belgium wasa.
A baya bayan nan ne Lukaku ya janye kansa daga buga wasannin da ƙasarsa Belgium za ta buga, don mayar da hankali kan farfaɗowa daga doguwar jinya da ya tafi bayan raunin da ya samu a Napoli.
Sai dai kasancewar ya fara samun sauƙi yanzu, ɗanwasan mai shekaru 32 ya ƙi bin shawarar kocin Napoli, Antonio Conte da jami’an ƙungiyar kan ya koma yin atisaye a can kamar yadda ya kamata.
A halin yanzu, ana raɗe-raɗin cewa ƙungiyar za ta iya ɗaukar matakin ladabtarwa kan Lukaku, saboda saɓa wa ƙa’idojin ƙungiyar kan halayyar ‘yanwasanta da ke farfaɗowa daga jinya.
Yanayi mai haɗari
Ko da ya zaɓi zama a birnin Antwerp na Belgium, Lukaku na yin atisaye a wani asibiti na musamman, inda shi ma wani ɗanwasan Belgium da Napoli, Kevin De Bruyne ya yi jinya. Amma saɓanin De Bruyne, Lukaku bai samu izinin kulob ba.
Yanayin da yake ciki na da haɗari ga makomar Lukaku, kasancewar a gabaɗaya kakar bana ta 2025-26, mintuna 64 kawai ya buga a wasanni bakwai da aka saka shi, inda ya ci ƙwallo guda tak.
Ana tunanin cewa rashin kuzarinsa ne babban dalilin da ya sa ya ƙaurace wa tawagar Belgium a wasannin da za ta buga na sada zumunta da Amurka da kuma Mexico.
Haka nan, rashin buga wasa a Napoli zai iya yin mummunan tasiri kan damar Lukaku ta buga wa ƙasarsa, yayin da ya rage watanni kaɗan a fara gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026.
A Belgium dai, Romelu Lukaku shi ne ɗanwasan da ya fi kowa cin ƙwallo, da ƙwallaye 89 cikin wasanni 124.













