Hukumomin Jihar Zinder a Jamhuriyar Nijar sun kama wani mutum mai shekaru 25 da ake zargi da amfani da wuƙa wajen kai hare-hare ga mata da ke tafiya su kaɗai, kamar yadda 'yansanda suka tabbatar.
Nasarar kamen ta biyo bayan shafe makkoni ana samun ƙorafe-ƙorafe game da fashi da makami wanda mahara a kan babura ke kaiwa.
Yanayin ya dauki hankali ne sakamakon wani sabon rahoto da aka samu na wani mummunar hari a ranar 14 ga Maris, 2026, wanda hakan ya haifar da bincike cikin gaggawa.
Jami’an ‘yansanda sun kama wanda ake zargin ne bayan samame da tattara bayanan sirri da suka gudanar, inda suka gano maharin a cikin birnin Zinder, a cewar hukumomi.
Rahotannin sun bayyana cewa, a yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin kai hare-hare da dama kana ya bayyana cewa ba shi kaɗai ba ne ya ke kai hare-haren, har da wani abokinsa wanda kawo yanzu ba a san inda yake ba.
Jami'an tsaro suna kan neman abokin nasa ruwa-a- jallo.
Masu bincike sun ce maharan suna amfani da wani tsari na hawa babur, za su kai hari ga mutane, musamman ‘‘mata da ke tafiya su kadai a wuraren da babu mutane ko zirga-zirga sosai, sai su kai musu hari da wuka su kuma sace kayansu kamar jakunkuna da wayoyin hannu.
Ana zargin wanda aka kama da hannu a hare-hare kusan goma da aka kai rahotonsu, a hukumance aƙalla mutane shida da abin ya shafa sun tabbatar da cewa shi ne wanda ya kai musu hari, a cewar ‘yansanda.











