| Hausa
TURKIYYA
4 minti karatu
An fara taron Stratcom 2026 a Istanbul yayin da hankalin duniya ke ƙara tashi da yaƙin watsa labarai
Jagorori daga ƙasashe 38 ne suka haɗu don tunkarar watsa labaran ƙarya da gangan, da yadda AI ke ƙara kankane komai, da rikice-rikice a sassan duniya, da nufin saita akalar tsarin duniya ƙarƙashin taken rikita lamura duniya da neman mafita.
An fara taron Stratcom 2026 a Istanbul yayin da hankalin duniya ke ƙara tashi da yaƙin watsa labarai
Mataimakin Shugaban Kasa na Turkiyya, Cevdet Yilmaz, yana jawabi a yayin shirin taron kolin Stratcom 2026, a ranar 27 ga Maris 2026 a Istanbul, Turkiyya. / AA
8 awanni baya

An fara Taron Duniya kan Dabarun Sadarwar (Stratcom Summit) na 2026 a ranar Juma’a a Istanbul, inda manyan jami’ai daga kasashe 38 suka hallara don tattaunawa kan yaƙi a Gabas ta Tsakiya da manyan matsalolin da ke fuskantar tsarin duniya.

Taron na kwanaki biyu, wanda Sashin Sadarwa na Turkiyya ya shirya daga 27 zuwa 28 ga Maris ta, zai samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa na Turkiyya Cevdet Yilmaz, da Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan da Daraktan Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa Ibrahim Kalin.

Ministoci goma sha ɗaya daga ƙasashe 10 za su kasance daga cikin sama da manyan jami’ai 60 da za su halarci taron.

A ƙarƙashin taken “Rikicewar Tsarin Duniya: Rikice-rikice, Labarai da Neman Tsari,” taron zai yi nazari kan matsalolin tsarin duniya da ke haifar da rikice-rikice da hanyoyin da yankuna daban-daban suke bi na dawo da zaman lafiya a matakin duniya.

“Dan’adam na buƙatar zaman lafiya, kuma zaman lafiya na bukatar adalci”

A jawabin bude taron, Mataimakin Shugaban Turkiyya Cevdet Yilmaz ya gargadi cewa ƙaruwar rashin tabbas a duniya, da yaƙe-yaƙe da watsa labaran ƙarya da gangan suna sauya tsarin siyasar duniya kuma suna nuna muhimmancin dabarun sadarwar a jagoranci.

Ya ce tsarin da duniya take bi bayan Yaƙin Duniya na Biyu yana fuskantar ƙalubale yayin da sauyin ikon yake haifar da ƙwarewar hukumomi, yayin da rikice-rikice masu alaka da tsaro, da tattalin arziki, da sauyin yanayi da ƙaura ke zama wasu dawwamammun matsaloli a siyasar duniya.

Yilmaz ya bayyana yakin Isra’ila-Amurka kan Iran a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyar yankin da na duniya, yana nuni da matsalolin jinƙai da na tattalin arziki, kuma ya ce Turkiyya na matsa lamba don tsagaita wuta nan-take ta hanyar tattaunawar diflomasiyya da shugaban ƙasa Recep Tayyip Erdogan ke jagoranta.

Har ila yau ya yi suka ga ayyukan Isra’ila a Gaza, da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, da Lebanon da Siriya da kuma killacewar da ake yi wa Masallacin Ƙudus a Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye, yana kira ga nuna ƙaƙƙarfaradawa daga ƙasashen duniya kan take dokokin ƙasa da ƙasa.

Ya yi gargaɗi cewa watsa labaran ƙarya da gangan da ƙirƙirar abuwa ta hanyar amfani da fasahar AI suna ƙara samun karɓuwa a rikice-rikicen zamani, yana mai cewa yaƙin watsa bayanai da takaita wa kafofin watsa labarai hanyoyin samun bayanai suna ƙara dagula hanyar samun sahihan bayanai.

Ya jaddada rawar diflomasiya ta Turkiyya take takawa, inda ya ambaci ƙoƙarin sasanta rikice-rikice daga na Rasha da Ukraine zuwa Afirka, kuma ya ce Ankara na daga cikin ƙalila da ke iya yin hulɗa da Gabas da Yamma.

“Duniya tafi ƙasashe biyar girma… Dan’adam na buƙatar zaman lafiya, kuma zaman lafiya na buƙatar adalci,” in ji Yilmaz, yana ƙarawa da cewa: “Muna nufin mu kasance masu adalci kuma masu ƙarfi.”

Ya kammala da cewa dabarun sadarwar yanzu suna da muhimmanci wajen rage haɗari kuma ya yi kira da a samu ƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, da kafafen watsa labarai, da jami’o’i da ƙungiyoyin farar hula.

“Ba harsashi ne kadai ke barazana ba, yaudara ma tana yi’

Burhanettin Duran ya ce taron, wanda “ya zama na duniya,” yana ƙara jan hankalin kasashen duniya.

“Za mu tattauna batutuwan amincewa a fannin dabarun sadarwa tare da ajandar duniya kuma mu yi zuzzurfan musayar ra’ayoyi cikin,” in ji Duran.

Ya ce taron na gudana ƙarƙashin taken “Rikicewar Tsarin Duniya: Rikice-rikice, Labarai da Neman Tsari,” wanda ke nuna yanayin tashin hankali da halin da duniya ke ciki a yanzu.

“A wannan zamani da muke ciki, ba za a iya raba dabarun sadarwa da yankunan da ake rikice-rikice ba,” in ji shi, yana ƙarawa da cewa bayanai sun koma daga kawai isar da gaskiya zuwa wani makami na samun iko da gogayya.

“A yau, barazana ba da tankoki kawai take shigowa ba, tana shigowa da sabbin salo, kuma ba da harsasai kawai take zuwa ba har ma da yaudara tana zuwa,” in ji Duran, yana jaddada cewa kare gaskiya ya zama muhimmi kamar kare iyakokin ƙasa a sabon tsarin tsaro da yake bayyana.