Rahotanni daga ƙungiyar Santos ta Brazil na cewa gwarzon ɗanwasan ƙungiyar kuma tauraron tawagar Brazil, Neymar Jnr, ya samu saɓani da matashin ɗanwasa Robinho Jnr.
Mai shekaru 34, Neymar ya yi sa-in-sa da ɗan tsohon gwarzon ɗanwasan tawagar Brazil, Robinho yayin wasan atisaye.
Robinho babba, wani gwarzon ɗanwasa ne da shi ma ya buga wa Santos, da kuma ƙungiyoyin Real Madrid, Manchester City, Milan, da Basaksehir ta Turkiyya.
Neymar ya zargi matashin ɗanwasan mai shekaru 18 da yi masa yanka na raini, inda rahotanni suka ce ya harzuƙa har ya mari Robinho Junior.
Daga nan ne sai aka samu tunkuɗe-tunkuɗe tsakaninsu, sannan aka bai wa hammata iska kafin daga bisani Neymar ya huce har ya bai wa Robinho Junior haƙuri.
Sai dai wasu rahotanni na cewa Robinho Junior bai haƙura ba. Hasali ma, mashawartansa na neman ƙungiyar Santos ta fitar da sanarwa kan lamarin.
Baya ga batun faɗa tsakanin ‘yanwasa, Santos na fama da raunin tagomashi, inda take a mataki na 16 a teburin gasar Serie A ta Brazil.
Duk da cewa Neymar bai buga wasanni biyu na ƙarshe a ƙungiyar ba, zuwa yanzu ya ci ƙwallo huɗu da tallafin ƙwallo uku a wasanni 11 da ya buga.
Haka nan, har yanzu yana fatan samun gurbi a tawagar Brazil da za ta wakilci ƙasar a gasar Kofin Duniya na FIFA 2026 da za a yi a Amurka, Mexico, da Canada.









