Dakarun haɗin gwiwa na Operation HADIN KAI da ke aiki a arewa maso gabashin Nijeriya daƙile harin ISWAP a sansanin sojin Nijeriya na Mandaragirau a Jihar Borno, inda suka kashe ‘yanta’adda 38 tare da kwato makamai.
A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, wadda Laftanar Kanal Sani Uba, Jami’in Watsa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta OPHK ya sanya wa hannu, sojojin sun fafata da maharan ta bayan yi musu “kwanton-ɓauna mai kyau da kuma tsare-tsaren kai hari da kare kai da suka tilasta musu janyewa cikin rudani.”
Haka kuma, ɓangaren sojojin sama ya bayar da goyon baya ta hanyar hare-hare daga sama da kuma bayanan leƙen asiri domin inganta hare-hare.
Bayan haka, an ci gaba da bin sawun maharan a hanyoyin da suka bi yayin janyewa inda hakan ya jawo musu ƙarin asara mai yawa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Jumullar ‘yan ta’adda kusan 38 aka kashe, inda aka gano gawawwaki 8 a yankin da aka yi arangama kai tsaye, sannan bayanan sirri daga mazauna yankin sun tabbatar da cewa akwai gawawwaki fiye da 30 da makamai da aka watsar a kan hanyar Garin Mallum zuwa Garin Gajere zuwa yankin Timbuktu Triangle. Hakan ya ƙara tabbata ne ta hanyar jinin da aka gani a hanya da kuma kayan aiki da suk watsar.”
Sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda bakwai, alburusai guda takwas, bam-bamai na RPG guda huɗu, da sauran alburusai daban-daban. Rundunar ta Operation Hadin Kai ba ta yi asarar rai ba, sai dai wata motar yaki kirar MRAP guda ɗaya ta samu matsala sakamakon harin RPG, inda aka yi gaggawar kula da waɗanda suka ji rauni.
Sanarwar ta nuna cewa girman asarar da maƙiyan suka yi “ta haifar da farin ciki sosai a tsakanin al’ummomin yankin, kuma hakan ya nuna yadda sojojin OPHK ke ci gaba da rinjaye wajen hana ‘yan ta’adda samun damar yin ayyukansu.”
A halin yanzu, ana ci gaba da ayyukan bin diddigi a kan hanyar Garin Mallum zuwa Garin Gajere domin tattara gawawwaki da kuma ƙarfafa nasarorin da aka samu.








