Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta bayyana shirinta na toshe dukkan layukan waya da ake amfani da su wajen ayyukan damfara a fadin kasar, kamar yadda Shugaban hukumar Aminu Maida ya bayyana ranar Alhamis.
Wannan mataki na daya daga cikin kokarin hukumar na karfafa tsaro a fannin fasahar zamani da kuma dawo da amincewar jama’a ga tsarin sadarwa na kasar, a cewar shugaban.
Yunkurin Kare Bayanan Sirri
Babban Shugaban Aminu Maida, ne ya sanar da hakan yayin wani taro na masu ruwa da tsaki kan Tsarin Sarrafa Bayanan Sadarwa (TIRMS) da aka gudanar a Abuja.
Rimini Makama, Kwamishiniyar Gudanarwa ta Hukumar, wadda ta wakilci Aminu Maida, ta bayyana cewa wannan yunkuri ya biyo bayan yadda ake yawan amfani da layukan waya ta hanyar da ba ta dace ba.
Ta bayyana cewa layukan da ake sake sayarwa, da waɗanda aka sauya bayan sun ɓata, ko kuma waɗanda ba a yi wa rajista yadda ya kamata ba, sun zama manyan makaman da miyagu ke amfani da su wajen damfarar kudi da satar bayanan sirri na mutane.
Don magance wadannan kalubale, NCC ta gabatar da wani tsari na doka da duka masu ruwa da tsaki za su yi amfani da shi wanda zai bai wa kamfanonin sadarwa, da bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi da sauran muhimman sassa damar tantance ingancin layukan waya da ake da alamar zargi a kansu kafin su amince wa mai layin yin hulda da shi ko samun wasu ayyuka daga wajensu.
Matakan da za a bi kafin toshe layi
A matsayin wani ɓangare na wannan sabon tsarin, NCC na shirin yi wa Dokokin Ingancin Aiki da na Rijistar Masu Amfani da Layi gyaran fuska.
Wasu daga cikin sababbin dokokin sun tanadi cewa dole ne kamfanonin sadarwa su sanar da mai amfani da layi a kalla kwanaki 14 kafin su toshe layin idan ba ya amfani da shi.
Dole ne kamfanoni su miƙa dukkan bayanan layukan da aka daina amfani da su zuwa dandalin TIRMS cikin kwanaki 7 bayan kammala toshe su.
Sai kuma samar da tsayayyen tsari na toshe layukan da aka gano an yi rajistarsu ta hanyar zamba ko ake amfani da su wajen aikata laifuka.








