Gwamnatin Nijeriya ta sanar da fara amfani da sabuwar allurar riga-kafin ƙwayar cutar HIV mai suna Lenacapavir. Allurar Lenacapavir tana aiki mai dogon zango don hana ƙwayar cutar HIV.
Wannan sabon shirin wani ɓangare ne na muradun kawar da cutar HIV/AIDS, kuma yana da burin cire cutar daga jerin manyan cututtuka masu girman barazana, nan da shekarar 2030.
Ma'aikatar Lafiya da Walwalar Jama'a ta Nijeriya, ƙarƙashin Ministan Dr Muhammad Ali Pate, ke jagorantar shirin, kamar yadda Ministan ya sanar a Abuja, babban birnin ƙasar.
Shirin riga-kafin zai samu tallafin Hukumar Wayar da Kan Jama'a ta Nijeriya, National Orientation Agency (NOA), don tabbatar da nasararsa, da tasirinsa ga kiwon lafiya.
Tun da fari, an zaɓi Nijeriya ta zama ɗaya cikin ƙasashe tara da za a fara amfani da sabuwar allurar riga-kafin HIV. Tuni dai aka karɓo adadin allurar 52,000 don fara ba da ita a faɗin ƙasar.
Saɓanin alluran da ake bai wa masu fama da cutar HIV/AIDS, wannan allurar riga-kafin ana ba da ita ne sau biyu a shekara kacal.
Masana kiwon lafiya suna cewa rage yawan buƙatar shan magani zai taimaka wa waɗanda ke shan wahalar jure wa shan magani HIV/ AIDS na kullum-kullum kamar na ART.
Kididdiga ta nuna cewa Nijeriya na da masu ɗauke da cutar HIV/AIDS har miliyan 1.9, kuma cutar na cikin manyan cututtukan da ke wahalar da masu ita musamman wajen magani da kuma walwalar rayuwa.
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya ta ƙaddamar da shirin riga-kafin HIV, na allurar Lenacapavir
Masana kiwon lafiya suna cewa rage yawan buƙatar shan magani zai taimaka wa waɗanda ke shan wahalar jure wa shan magani HIV/ AIDS na kullum-kullum kamar na ART.

Rumbun Labarai






