Zahra Arghavan da Mehdi Alishir suna tsaye a barandar benensu, suna kallon rana na faduwa a samaniyar Tehran sannan suna jin karar fashewar abubuwa saboda hari.
A yayin da lokaci ke ƙara kusantowa a wa’adin da Trump ya bayar, ƙwaƙwalensu sun cika da fargaba da tsoro: Har zuwa yaushe ne lantarkin zai zama a yanke idan aka kai wa cibiyoyin harin bam? Ta yaya za su fita daga birnin idan aka rusa gadoji?
Makonni biyar ke nan, sun saba da jin karar jiragen yaki da fashewar abubuwa a hare-haren da Amurka-Isra’ila ke kaiwa, sautin na hana su bacci.
Kamar wasu da dama, su ma sun bar birnin amma sun sake dawo wa don neman matsira. Sun yi aure sama da shekaru 10 da suka gabata, sun tsira da rayuwarsu lokacin annobar Covid-19 da watan Yunin bara.
Sun yi amfani da salatif don manne gefen tagoginsu don kare su daga fashewa bayan an kai hari. An boye madubi da gilasai da ma abubuwan fashewa a waje mai tsaro. Sun tanadi jaka dauke da takardu da magunguna, ko da a ce za su bukaci guduwa cikin gaggawa.
A wata barazana da ya yi karara a karshen makon da ya gabata Trump ya ce zai fara kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati da fararen hula daga ranar Talata idan Iran ba ta bude Mashigar Teku ta Hormuz ba, kuma ‘yan Iran za su ‘Rayu a Wuta’.
“Gaskiya yanayin ya rikice baki daya” in ji Arghavan. “Ba mu fahimci abubuwan ba kamar zuwa yaushe ne lantarki zai katse, kuma yaya rayuwa za ta kasance idan babu lantarki.”
Alishir ya ce shi da matarsa ba za su iya rayuwa sama da sati daya babu wuta da ruwan famfo ba.











