| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Iran ta ce Mashigar Teku ta Hormuz a bude take ga duniya, amma a rufe ga maƙiya
Mai bayar da shawara ga Shugaban Addini na Iran Velayati ya bayyana cewa yakin Isra’ila-Amurka zai kawo karshe ne duba ga sharuddan Iran a yayin da Iran din ke ci gaba da rike iko da Mashigar Teku ta Hormuz mai muhimmanci.
Iran ta ce Mashigar Teku ta Hormuz a bude take ga duniya, amma a rufe ga maƙiya
Har yanzu "Kasashen Abokai" na samun damar wuce wa ta mashigar tekun Hormuz, in ji Iran. [File photo] / AA / AA

A ranar Alhamis Iran ta bayyana cewa Mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a bude ga jiragen ruwa na duniya amma "a rufe" ga maƙiyanta da sansanoninsu na yankin.

Ali Akbar Velayati, mai ba da shawara ga Jagoran Addini na Iran Mojtaba Khamenei, ya fada a cikin wani jawabi da ya yi a shafin sadarwar yanar gizo na X cewa sakamakon yakin zai dogara ne da sharuddan da Iran za ta gindaya maimakon abin da ya bayyana a matsayin "mafarkin" maƙiyanta.

"Mashigar Hormuz a bude take ga duniya, amma za ta ci gaba da kasancewa a rufe ga maƙiyan mutanen Iran da sansanoninsu a yankin," in ji shi.

Velayati ya kara da cewa yakin zai ƙare bisa ga sharuddan Iran.

"Yaƙin zai ƙare da manufofin Iran da ikonta, ba tare da maye da ruɗani na masu kai hari ba," in ji shi.

Jawabinsa ya zo ne sa'o'i bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a cikin wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin daga Fadar White House cewa Iran tana da jiragen harba makamai masu linzami "ƙalilan" da suka rage kuma an "rage karfin ikonta na harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa."

Trump ya ce yana sa ran yakin zai ci gaba na tsawon wasu makonni biyu zuwa uku amma yana ganin rikicin na gab da zuwa "ƙarshe."

Tehran ta ci gaba da kula da mashigar teku ta Hormuz, wata hanya mai mahimmanci ta jigilar makamashi ga ƙasashen Asia, wanda hakan ya ba jiragen ruwan waɗannan ƙasashen da Iran ke kira "ƙasashe masu aminci" damar wucewa.

Tsaron da ake yi a yankin ya ƙaru tun lokacin da Isra'ila da Amurka suka ƙaddamar da wani hari na haɗin gwiwa kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 1,340, ciki har da Jagoran Addini na wancan lokacin Ali Khamenei.

Iran ta mayar da martani da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami da aka kai wa Isra'ila, Jordan, Iraki da ƙasashen Gulf waɗanda ke ɗauke da kadarorin sojojin Amurka, wanda ya haifar da asarar rayuka da lalacewar kayayyakin more rayuwa yayin da yake kawo cikas ga kasuwannin duniya da safarar jiragen sama.

Rumbun Labarai
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
Araghchi ya faɗaɗa zirga-zirgar diflomasiyyar Iran daga Islamabad zuwa Moscow
Sisi na Masar ya yi gargaɗi kan 'ƙoƙarin da ake yi da gangan' na sake zana taswirar Gabas ta Tsakiya
Falasɗinawa na kaɗa ƙuri'a a zaɓen farko tun bayan yaƙin ƙare-dangi da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza
Iran ta ce ba kai-tsaye za a yi tattaunawa a Pakistan don kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila ba
Turkiyya da ƙasashe bakwai sun soki Isra'ila kan keta alfarmar Masallacin Ƙudus
Trump ya fasa kai wa Iran hari da makamin nukiliya
Daraktan IEA ya ce ana asarar gangar mai miliyan 13 kullum saboda rufe Mashigar Hormuz
Amurka ta dakatar da jigilar dala zuwa Iraƙi, amma me ya sa take aika kuɗi zuwa Baghdad?
Trump ya tsawaita tsagaita wutar Iran domin bai wa Tehran ƙarin lokaci na tattaunawa
Vance zai tafi Pakistan ranar Talata domin tattaunawa da Iran  — rahoto
Sojan Isra’ila na shan suka bayan ya lalata mutum-mutumin Yesu a Lebanon
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan jiragen Amurka a kan ƙwace jirgin dako: Rahoto
Isra'ilawa da dama sun mamaye Masallacin Ƙudus a ƙarƙashin rakiya da tsaron 'yansanda mai tsanani
Trump ya ce Amurka na yin tattaunawa mai kyau da Iran, ya yi gargaɗi kan rufe Mashigar Hormuz
Hare-haren Iran sun lalata fiye da gidaje 1,000 tare da mayar da su kufai a Tel Aviv - Magajin Gari
Iran ta kama mutum 127 kan zargin taya abokan gaba shirya kai mata hari ta ƙasa
Trump ya ce za a yi amfani da ‘manyan katafilolin tone kasa’ don kwashe sinadarin Uranium daga Iran
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya
Jakadan Iran a MDD ya bayyana ƙawanyar Amurka a matsayin 'matakin tsangwama'