Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya ta bayyana cewa shari’ar da ke yi a wata kotun Gundumar Columbia ta Washington a Amurka ana yin ta ne game da jayayya kan fitar da bayanai ba wai shari’ar laifi kan Shugaba Bola Tinubu ba.
Wata sanarwar da mai bai wa shugaban Nijeriyar shawara kan watsa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar ta ƙara da cewa babu wata kotun da ta sami shugaban da laifi.
“Wannan shi ne bayani game da shari’ar, wadda ke zuwa shekara 23 bayan ofishin jakadancin Amurka a Legas, a wata wasiƙar da ta rubuta ranar 4 ga Fabrairun shekarar 2003, ta bayyana wa Babban Sufeton ‘Yansandan na wancan lokacin, Mista Tafa Balogun, cewa wani binciken bayanan Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ba ta sami tarihi na kamu ko sammaci na aikata laifi kan gwamna Bola Ahmed Tinubu na wancan lokacin ba,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa a shekarar 2022, Mista Aaron Greenspan, wanda aka sani da aiki da ‘yan adawar Nijeriya ciki har da David Hundeyin da Atiku Abubakar, sun gabatar da buƙatar aiki da Dokar Samun Bayanai ga wasu hukumomin inda suke neman bayanai game da Shugaba Tinubu.
“Bayan hukumomin sun riƙe wasu bayanai ko kuma ƙin tabbatar da ko kuma musanta kasancewarsu, Mista Greenspan ya shigar da shari’ar neman haƙƙi mai lamba 23-1816 a gaban kotun ta Amurka ta Gundumar Columbia a shekarar 2023,” in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta ce kotun ta bai wa Shugaba Tinubu damar shiga shari’ar a matsayin mai ruwa da tsaki a shari’ar.
Yayin zaman kotun, waɗanda aka kai ƙarar sun gabatar da wata irin kariya mai nuna cewa hukumar gwamnatin ba za ta iya musanta ko kuma amince da kasancewar binciken ba, in ji sanarwar tana mai cewa wannan na kare jami’an hukumomin tsaro da dabaru da kuma majiyoyin da suke amfani da su wajen bincike da kuma gurfanar da laifuka a kotu.
Bisa ga amfani da irin wannan kariyar, kotun Gundumar ta Amurka ta yanke hukuncin da ya bai wa hukumomin CIA da EOUSA da ma’aikatar harkokin wajen Amurka da hukumar tattara harajin Amurka (IRS) nasara, in ji Onanuga.
“Kotun ta yanke hukuncin cewa a cire su daga shari’ar, inda ta bar wasu ɓangarori na ikirarin da ke da alaƙa da Hukumar Binciken Laifuka ta Tarayyar Amurka (FBI) da kuma Hukumar Da ke Yaƙi da safarar miyagun ƙayoyi (DEA) domin ƙarin nazari,” a cewar sanarwar.
Daga nan sai hukumomin FBI da DEA suka ba da rahoto mai shafi 399 inda suka rufe wasu ɓangarori na rahoton, lamarin da masu shigar da ƙara suka ƙalubalanta, a cewarsa.
Sai dai kuma FBI da DEA sun yi watsi da buƙatar bayar da bayanan ba tare da riƙe wasu ɓangarorinsu bisa wasu dalilai biyar ba, in ji sanarwar.
“Masu shigar da ƙarar suna da lokaci zuwa ranar 11 ga watan Satumba na shekarar 2026, domin shigar da adawarsu kuma su mayar da martani ga waɗanda aka kai ƙarar da wanda ya shiga shari’ar daga baya, yayin da FBI da DEA da wanda ya higa shari’ar daga baya ke da lokaci zuwa ranar 18 ga watan Satumba na shekarar 2026 su mayar da martani ga ƙarar da masu shigar da ƙarar za su shigar,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa fitar da ko kuma riƙe bayanai a ƙarƙashin Dokar Neman ‘Yancin Bayanai ba ya nufin tabbatar da aikata laifi.
“Shari’ar tana da alaƙa ne da damar samun bayanan gwamnati da kuma ɗabbaka dokar keɓe wasu abubuwa yadda ya dace,” in ji sanarwar.
Ta kuma yi kira ga kafafan watsa labaran Nijeriya su gane cewa wannan shari’ar tana hannun maishari’a Beryl A. Howell ta Kotun Gunduma na Amurka ne.
“Ita za ta tabbatar da sakamakonta, bisa hujja da doka da kuma bayanan waɗanda ke da ruwa da tsaki a shjari’ar, ba burin da Alhaji Atiku Abubakar ko wakilinsa, Msita Von Batten, ya fi so ba,” in ji sanarwar.

























