Aƙalla shaguna 300 ne suka ƙone a wata mummunar gobara da ta tashu a babbar kasuwar Oranyan da ke birnin Ibadan na jihar Oyo a Nijeriya, lamarin da ya jawo mummunar asara ga ‘yan kasuwa waɗanda ke neman taimakon gwamnati cikin gaggawa.
Gobarar ta tashi ne da tsakar daren ranar Lahadi zuwa wayewar Litinin kuma ta bazu zuwa sassa da dama na kasuwar da ke yankin karamar hukumar Arewa maso Gabashin Ibadan, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Oyo ta ce gobarar ta fara ne daga tsakiyar kasuwar bayan fashewar wani abu. Ko da yake, hukumomi ba su tabbatar da ko fashewar iskar gas ne ko kuma wani abu na daban ba.
Shugaban Hukumar ta Jihar, Moruf Akinwande, ya ce jami’an kashe gobara sun shawo kan lamarin, inda suka yi ƙoƙarin hana bazuwar wutar zuwa wasu sassan kasuwar.
Haka kuma ya ce, jami'ai sun ƙaddamar da bincike tare da tattara cikakkun bayanai game da adadin shagunan da lamarin ya shafa da kuma darajar yawan kayayyakin da suka ƙone.
Lamarin ya sake haifar da fargaba game da sake afkuwar gobarar kasuwa a Ibadan da kuma irin asarar da 'yan kasuwa ke tafkawa mussamman wadanda rayuwarsu ta dogara ga cibiyoyin kasuwanci na birnin.
Wata babbar gobara ta taba tashi a kasuwar Oranyan a shekarar 2024, lamarin da ya kona shaguna da dama a sashen kasuwar na sayar da magungunar gargajiya.
Lamarin na baya-bayan nan ya faru ne kwana biyu kacal bayan rahoton wata gobara da ta lakube wasu shaguna guda tara a Cibiyar Siyayya ta Jirgin Kasa ta Nijeriya kusa da ke cikin Kasuwar Aleshinloye a Ibadan.
Yawan gobarar da ake samu na buƙatar ƙara daukar matakan kariya kan aukuwar gobara da inganta hanyoyin daukar matakan gaggawa da kuma sa ido sosai kan tsaro a kasuwanni a faɗin birnin.
Yayin da 'yan kasuwa ke tantance asarar da suka yi, hankali ya koma kan Gwamnatin Jihar Oyo da sauran hukumomin da abin ya shafa don neman taimako.
Bayan agajin gaggawa, 'yan kasuwar da abin ya shafa suna buƙatar tallafi don sake gina shagunansu da kuma dawo da kasuwancin da gobarar ta tarwatsa, a cewar shugaban ‘yan kasuwar.



















