Masu garkuwa da mutane a Nijeriya sun tara aƙalla naira biliyan 7 (kwatankwacin $5.79 miliyan) na kudin fansa tsakanin watan Yulin 2025 zuwa Yunin 2026, a cewar wani rahoton bincike na kamfanin tattara bayanan tsaro na SBM wanda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya rawaito.
Rahoton ya ce an yi garkuwa da mutum 7,825 a tsakanin wannan lokacin, adadin da ya kai karuwar kashi 66 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Sannan an kashe akalla mutane 1,142, kuma jimillar kudin fansa da aka biya ya ninka sau uku zuwa Naira biliyan 7.78 ($5.79 miliyan), in ji rahoton.
Binciken na SBM ya nuna alƙalluman da aka tattara daga rahotannin kafofin watsa labarai da hirarraki da kuma bayanai da aka samu daga al'umma, ba su bayyana takamamman yawan adadin kuɗin fansa da aka biya waɗanda aka sanar ba.
Ƙungiyar ‘yanta’adda ta Boko Haram ita ke da kusan kashi 90 cikin 100 na kudaden fansa da aka biya daga yankin arewa maso gabashin Nijeriya, yayin da arewa maso yamma ta sami mafi yawan mutane da aka yi garkuwa da su da kuma waɗanda abin ya shafa.
Rahoton SBM ya kiyasta cewa Boko Haram ta samu kimanin naira biliyan 7, galibi daga wasu manyan harin garkuwa da mutane biyu da suka faru inda aka sace fiye da mutane 300 ko wannensu.
Ɗaya daga cikin manyan harin ya faru ne a watan Nuwamba, inda aka sace dalibai da ma'aikata 315 daga wata makaranta a Papiri da ke Jihar Neja.
Rahoton ya ce sake bullar yanayin garkuwa da dalibai a makarantu na ƙara matsin lamba ga sha’anin ilimi da yanayin rayuwa da kuma yarda da gwamnati.
Binciken ya zo ne yayin da Shugaba Bola Tinubu ya umarci jami'an tsaro da su ceto mutane har 600 da aka ce an sace a Jihar Neja a makon da ya wuce.
Garkuwa da mutane don neman ƙuɗin fansa ya kasance babban ƙalubalen tsaro a Nijeriya, inda 'yan fashi da makami da kungiyoyi ‘yata’adda ke kai hari kan makarantu da ƙauyuka da kuma manyan hanyoyi.
Binciken na kamfanin SBM Intelligence ya yi gargaɗin cewa, idan ba a samar da hanyoyin da suka dace don rage irin ribar da ake samu daga ƙuɗaɗen fansa da ake biya masu garkuwa da mutane ba tare da magance matsalolin da ke haifar da hakan, to babu shakka wannan mummunar laifi zai iya zama tushen samun kuɗi mai ɗorewa ga ƙungiyoyin ‘yanbindigida.
Ana sa ran tsaro zai ci gaba da zama babban batu da za a fi mayar da hankali akai kafin babban zaɓen Nijeriya da ke tafe a watan Janairun 2027.





















